2019: Su wanene za su zama Ministocin Buhari daga irin su Kano da Katsina

2019: Su wanene za su zama Ministocin Buhari daga irin su Kano da Katsina

A halin da ake kicin-kicin ganin wa'adi na biyu kuma na karshe na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, mun kawo jerin jihohin da ake tunani za a iya kai ruwa rana kafin a zabo Ministoci

1. Adamawa

Jam’iyyar APC tana da manyan ‘yan siyasa daga jihar Adamawa irin su Nuhu Ribadu, Buba Marwa, Tukur Halilu wanda duk za su rai shugaba Buhari zai ba su wani mukami ganin irin dawainiyar da su kayi wa jam’iyyar. Bayan wannan kuma shi karan kan-sa Gwamna Jibrila Bindow ya sha kasa a zaben 2019.

2. Akwa Ibom

A jihar Akwa-Ibom, shugaba Buhari zai zabi wanda zai ba Minista tsakanin tsohon Gwamna Godswill Akpabio wanda ya sha kasa a zaben Sanatan bana, Akpabio yayi wa APC kokari a zaben 2019, da Hadimin Shugaban kasa Ita Enang, ko kuma shugaban kasar ya cigaba da aiki da Ministansa na kasafi Udo Udoma.

KU KARANTA: Wannan karo ka zakulo kwararru - Bakare ya ba Buhari shawara

3. Bauchi

A jihar Bauchi ma dai Jam’iyyar APC tana da ‘ya ‘yan da ake ji da su irin su Dr. Mohammed Ali Pate, Yusuf Tuggar da sauran su. Ciwon kai zai karu ga shugaba Buhari ne bayan gwamnan APC a jihar watau Mohammed Abubakar ya rasa kujerarsa. Na-hannun daman shugaban kasa watau Adamu Adamu shi ne Minista daga jihar.

4. Kano

Daf da zaben 2019 jam’iyyar APC ta karbi manyan ‘yan adawa na PDP a Kano. Daga ciki akwai Ibrahim Shekarau wanda ya lashe kujerar Sanata da kuma irin su tsohon mataimakin gwamna Hafiz Abubakar, Aminu Dabo, da sauran su. Kano na cikin inda za a zura idanu wajen ganin wanda za a dauko a matsayin Minista a 2019.

5. Katsina

Haka zalika akwia kallo a jihar shugaban kasa watau Katsina, inda manyan Sanatocin jihar guda 2 ba su koma kujerarsu ba; Sanata Abu Ibrahim ya hakura da takara a bana inda ake tunanin yana harin Minista, sannan kuma Umaru Kurfi ya sha kashi. A halin yanzu jama’a su na ganin cewa Hadi Sirika yana dasawa da shugaban kasa.

KU KARANTA: Iyalin Shugaba Buhari su ka sa Gwamnan APC ya sha kasa a 2019

Akwai kuma manyan ‘yan PDP da ke jirin sakayya irin su Musa Nashuni, Umaru Tata, Abdullahi Garba Faskari da sauran su wanda duk sun dawo tafiyar jam’iyyar APC a daidai lokacin da ake shirin zaben 2019.

6. Zamfara

Jihar Zamfara tana cikin inda APC ke fama da rigingimu kaca-kaca, yanzu haka dai har batun zaben cikin-gida na jam’iyyar ya kai gaban kotun koli, inda gwamna mai-ci ya samu sabani da manyan ‘yan jam’iyya har 8 da ke neman gwamna daga ciki akwai Sanata mai-ci, Dan majalisa, Minista, tsoho da kuma mataimakin gwamna na jihar mai-ci.

7. Legas

A jihar Legas, shugaba Buhari zai yi fama inda APC ta hana gwamnan ta mai-ci watau Akinwumi Ambode tuta. Duk da irin kokarin gwamnan, zai fice ya ba Jide Sanwo-Olu wuri a Watan gobe. Sai dai kuma gwamnan mai shirin barin-gado zai gamu da cikas wajen samun irin kujerar da tsohon gwamna Tunde Fashola yake rike da ita a yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel