'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda uku da mai unguwa

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda uku da mai unguwa

- Wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an hukumar 'yan sanda guda uku , da wani mai unguwa

- Rundunar 'yan sandan jihar ta kama mutane 69 wadanda ta ke zargi da hannu a kisan

Wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya guda uku da kuma mai unguwar Iriebe, a karamar hukumar Oyigbo da ke jihar Rivers.

'Yan bindigar sun kai hari garin a ranar Larabar nan da ta gabata, inda suka shiga garin da bindigogi da adduna, suna yi wa al'ummar Hausawa da ke garin barazana.

Jami'an tsaron yankin sun kai wa 'yan bindigar hari, inda suka samu nasarar kashe biyu daga cikin 'yan ta'addar.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda uku da mai unguwa

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda uku da mai unguwa
Source: UGC

A wani abu mai kama da daukar fansa, wasu daga cikin 'yan ta'addar sun sake hada gayya suka sake kai hari garin, inda suka kashe 'yan sanda biyu da kuma mai unguwa.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa 'yan bindigar sun sake harbe wani dan sandan ranar Alhamis dinnan, hakan ya sanya yawan 'yan sandan da aka kashe din ya zama guda uku.

Mai garin Iriebe, wanda aka kashe dan'uwansa, Jeremiah Worenwu, ya ce kusan mako daya kenan ana ta faman samun tashin hankali a yankin, tun bayan lokacin da 'yan sanda suka sanar dashi cewa wasu matasa sun kwaci bindigogi a hannun 'yan sanda a garin.

KU KARANTA: Hotuna: Yanzun nan shugaba Buhari ya isa jihar Borno

Amma matsalar tsaro a yankin ya kara muni bayan da 'yan sanda suka gano wata maboya da matasan suka boye bindigu a cikin garin.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar Nnamdi Omoni, ya ce 'yan bindigar sun kashe 'yan sanda guda uku.

Ya bayyana cewa an kama mutane 69 wanda ake zargin su da hannu cikin kisan, yanzu haka an tura su ofishin binciken manyan laifuka, domin kara tabbatar da bincike akan su.

"Yanzu komai ya dawo dai dai a yankin mutane kowa ya koma harkokinsa, wadanda suka gudu kuma zasu iya dawowa," in ji Omoni.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel