Na yaba da kwazon aiki na gwamnan jihar Borno Shettima – Buhari

Na yaba da kwazon aiki na gwamnan jihar Borno Shettima – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna gamsuwa da ayyukan da Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ya aiwatar a shekaru takwas da suka gabata.

Shugaban kasar wanda ya kai ziyarar aiki na kwana daya Maiduguri, babbar birnin jihar Borno ya nuna farin ciki matuka da zabin ayyukan Shettima a fannin ilimi, lafiya, noma da kuma hanyoyi wanda ya kaddamar wa da mutanensa a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu.

Buhari ya bayyana hakan a ranar Alhamis a fadar Shehun Borno yayinda yake martani ga sarkin Bornon, Alhaji Abubakar Garbai Ibn El Kanemi da Gwamna Shettima.

Na yaba da kwazon aiki na gwamnan jihar Borno Shettima – Buhari

Na yaba da kwazon aiki na gwamnan jihar Borno Shettima – Buhari
Source: UGC

Shugaban kasar musamman ya nuna farin ciki da makarantun firamare da aka gida domin yara marayu da harin Boko Haram ya tagayyarar a jihar sannan ya nuna yakinin cewa babu makawa marayun za su samu ilimi mai inganci da makoma nagari.

Ya kuma nuna bakin cikin cewa har yanzu sauran yaran na a hannun yan ta’addan Boko Haram.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya karkashin kulawarsa zata yi duk abunda ya kamata domin ceto sauran yaran daga hannun Boko Haram.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya na sane da cewar gwamnatin jihar ta dauki nauyin karatun yan matan Chibok da aka sace a makarantun sakandare da jami’a daban-daban a ciki da wajen Najeriya doomin samun ingantaccen ilimi.

KU KARANTA KUMA: Abun da ya sa Buhari ba zai sauke ministocinsa ba – Lai Mohammed

Ya kuma nuna godiya ga mutanen Borno kan kulawarsa gare shi sannan ya yaba ma biyayyar da suka yi ma gwamnatinsa.

Buhari ya kuma jinjina ma gwamna Kashim Shettima akan namijin kokarin da yayi wa jiharsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel