Rayuwar sanata Adeleke na cikin hadari, jam’iyar PDP ta koka

Rayuwar sanata Adeleke na cikin hadari, jam’iyar PDP ta koka

-Akwai lauje cikin nadi bisa kama Abass Adejare a ganin jam'iyar PDP

-Jam'iyar APC tayi shirin yakar Adeleke ko ta halin kaka, a zargin jam'iyar PDP

Jam’iyar PDP ta sanar da 'yan Najeriya hadarin da rayuwar Adeleke take ciki. Adeleke dai shine dan takarar gwamna karkashin jam’iyar PDP a jihar Osun.

Jam’iyar tayi kira na a gaggauta sakin Kadili Adejare Abass wanda shine shugaban makarantar sakandaren da Adeleke ya gama.

Rayuwar sanata Adeleke na cikin hadari, jam’iyar PDP ta koka

Rayuwar sanata Adeleke na cikin hadari, jam’iyar PDP ta koka
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN:Majalisar dattijai ta ki amincewa da Kogi a matsayin jihar dake da man fetur

Da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja, sakataren hulda da jama’a na PDP Kola Ologbondiyan yace: “Abin zaiyi matukar baka mamaki ganin cewa wasu gurbatattu yan jam’iyar APC na son jefa Adeleke cikin halin tsaka mai wuya duk don su hana shi cinma nasara a kotu.

“Duba ga labarin hare-hare da kuma barzanar kisa dama wasu abubuwa daban-daban, jam’iyar dai ta APC ta lashi tokobin hana sanata Adeleke kaiwa ga matakin nasara ne a kotu wanda hakan zai iya bashi damar kasancewa a matsayin zababben gwamnan Osun.

“Daya daga cikin munanan ababen da aka shiryawa Adeleke, akwai kama shugaban makarantar Ede Muslim School. Inda akai mashi kagen cewa takardar shaidar kammala makarantar sakandare da Adeleke ke amfani da ita bata inganta ba.

“A jiyane ta hanyar hadin gwiwa tsakanin APC da hukamar ‘yan sanda aka damke Kadili Abass tare da matar daya daga cikin jagororin wannan makaranta da jaririnta dan wata 9 kacal da haihuwa.

“Babu yanda za’ayi ace shugaban makarantar da ya sanya hannu akan takardar kammala karatun ace kuma wai basu da inganci. Duk da shi ya tabbatar da sahihancin wadannan takardu.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel