Babu wani ma'aikaci da zai karbi albashin kasa da N30,000 a Najeriya

Babu wani ma'aikaci da zai karbi albashin kasa da N30,000 a Najeriya

- Kungiyar kwadago ta kasa ta gargadi dukkanin ma'aikatan Najeriya cewa kada wanda ya sake ya karbi albashin da ya yi kasa da N30,000 a kowacce jiha a kasar nan

- Kungiyar ta ce tunda har gwamnatin tarayya ta mayar da abin doka to ba wani uzuri da kowanne gwamna zai kawo na cewa ba zai iya biya ba

A jiya Alhamis ne 25 ga watan Afrilu kungiyar kwadago ta kasa ta gargadi cewa babu wata jiha a kasar nan da za ta karbi karancin albashi da ya yi kasa da N30,000.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa shugaban kungiyar kwadagon ta kasa, Mista Ayuba Wabba, shine ya fitar da sanarwar a garin Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti, yayin da yake jagorantar zaben shugaban kungiyar kwadagon na jihar.

Babu wani ma'aikaci da zai karbi albashin kasa da N30,000 a Najeriya

Babu wani ma'aikaci da zai karbi albashin kasa da N30,000 a Najeriya
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa kungiyar kwadago ta kasa ta bai wa ma'aikatan Najeriya umarnin kada su karbi karancin albashin da ya yi kasa da N30,000 daga wurin kowanne gwamna a Najeriya.

Wabba ya ce, sabon albashin ya zama wajibi gwamnoni su biya shi, tunda duka majalisun kasar nan guda biyu sun aminta da shi, kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akai ya mai da shi doka a kasar nan.

KU KARANTA: Hotunan: Yanzun nan shugaba Buhari ya isa jihar Borno

Ya ce kungiyar kwadago ba za ta taba karbar uzurin da wasu gwamnoni a kasar nan ke kawowa na nuna cewa baza su iya biyan albashin ba.

A wurin taron, inda tsohon shugaban kungiyar manyan ma'aikata na jami'ar jihar Ekiti, Mista Olatunde Kolapo, ya zama shugaban kungiyar kwadagon ta jihar Ekiti. Wabba ya ce ba za su yadda a canja sabon albashin ma'aikatan ba ta kowacce hanya ba a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel