Za a ragewa jami'an 'yan sanda lokacin aiki daga awanni 12 zuwa awanni 8 kowacce rana

Za a ragewa jami'an 'yan sanda lokacin aiki daga awanni 12 zuwa awanni 8 kowacce rana

- Shugaban hukumar 'yan sanda na rikon kwarya, IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin gaggawa akan ragewa jami'an 'yan sandan Najeriya lokacin aiki daga awanni 12 zuwa awanni 8

- Shugaban ya ce ya yi hakanne domin rage damuwa da gajiya dake tattare da ma'aikatan

Shugaban hukumar 'yan sanda na rikon kwarya, IGP Mohammed Adamu, ya umarci 'yan sandan fadin kasar nan da su dinga yin aikin sa'o'i takwas a kowace rana don rage musu damuwar da har ta ke kai su ga kashe mutane cikin ganganci.

Adamu ya bada umarnin ne a hedkwatar hukumar 'yan sandan, jiya Alhamis a Abuja, yayin wani taro da ya yi da shugabannin hukumar 'yan sandan na kasa, akan fannin lafiya na hukumar 'yan sandan.

Za a ragewa jami'an 'yan sanda lokacin aiki daga awa 12 zuwa awa 8 kowacce rana

Za a ragewa jami'an 'yan sanda lokacin aiki daga awa 12 zuwa awa 8 kowacce rana
Source: Original

An bude fannin lafiya na hukumar 'yan sandan ne a shekarar 1975, domin samarwa da jami'an 'yan sanda masu aiki da wadanda suka kammala aiki magunguna kyauta.

Yayin da yake jawabi, IGP ya ce ya bayar da umarnin rage lokacin aikin 'yan sandan ne, bayan la'akari da irin yadda jami'an suke daukar sa'o'i masu yawan gaske suna aiki, wadda hakan ke janyo musu gajiya sosai a tattare da su.

KU KARANTA: Hotuna: Yanzun nan shugaba Buhari ya isa jihar Borno

"Saboda haka, daga yanzu na yi umarnin canja tsarin aikin hukumar 'yan sanda daga sa'o'i 12 zuwa sa'o'i 8 a kowacce rana.

"Don kara tabbatar da tsaro, daga yau kada wani ma'aikacin hukumar 'yan sanda ya yi aikin da ya wuce na sa'a takwas a rana, sai dai idan bukatar hakan ta taso," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel