Dalilin da yasa ban hallara ba a lokacin ziyarar aiki da Buhari ya kai Lagas – Tinubu

Dalilin da yasa ban hallara ba a lokacin ziyarar aiki da Buhari ya kai Lagas – Tinubu

Asiwaju Bola Tinubu, babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu yace ba da gangan ya kaurace ma lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Lagas don kaddamar da ayyuka ba a ranar Laraba.

Ana ta rade-radin cewa Tinubu ya kaurace ma taron ne domin ramuwar gayya ga kin halartan bikin cikarsa shekaru 67 da Shugaban kasar bai yi ba a watan da ya gabata.

Sai dai da yake hira da jaridar Daily Independent, Tunde Rahman, mai ba Tinubu shawara a kafofin watsa labarai yace ubangidan nasa bai halarci taron bane saboda a yanzu haka baya cikin kasar.

Dalilin da yasa ban hallara ba a lokacin ziyarar aiki da Buhari ya kai Lagas – Tinubu

Dalilin da yasa ban hallara ba a lokacin ziyarar aiki da Buhari ya kai Lagas – Tinubu
Source: Facebook

“Asiwaju Bola Tinubu baya gari. A yanzu haka yana wajen kasar. Shiyasa bai halarci taron ba,” inji shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tun da jirgin da ya kawo shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya iso Legas, har ya koma, bai hadu da Asiwaju Bola Tinubu ba.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Arewa na cikin yaki – Marafa

Shugaba Muhammadu Buhari ya je Legas a ranar Laraba da misalin karfe 10:30 na safe har zuwa kusan 3:20 na yamma, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar a karkashin jagorancin gwamna Akinwunmi Ambode tayi.

Kamar yadda labarai su ka zo mana, babu wanda ya ga babban jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu wajen wannan ziyara da shugaban kasa ya kawo. Gwamnonin Kudu na yamma ne dai su ka tarbo shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel