Abun da ya sa Buhari ba zai sauke ministocinsa ba – Lai Mohammed

Abun da ya sa Buhari ba zai sauke ministocinsa ba – Lai Mohammed

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana cewa babu wani shiri da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a yanzu haka na sallamar ministocinsa daga bakin aiki.

Cikin makon jiya ne Shugaba Buhari ya umarci dukkan ministocin sa su aika da cikakken bayanin ayyukan da suka gudanar na tsawon wa’adin mulkin su.

Shugaban kasar ya umarce su da su aika takardar zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Wannan sanarwa da aka yi, ta sa an rika hasashen cewa babu mamaki Buhari ya shirya sauke ministocin na sa nan ba da dadewa ba, kafin ranar 29 ga watan Mayu, wanda yayi daidai da ranar sake rantsar da shi.

Abun da ya sa Buhari ba zai sauke ministocinsa ba – Lai Mohammed

Abun da ya sa Buhari ba zai sauke ministocinsa ba – Lai Mohammed
Source: Facebook

Sai dai kuma a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu, Lai Mohammed ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa cewa “Ministoci na nan daram, babu wani shirin tsige su ko sauke su da ake yi. Domin nan da ranar 22 Ga Mayu ba za mu yi taron yi wa juna bankwana da murnar kammala zangon 2015 zuwa 2019 lafiya.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Arewa na cikin yaki – Marafa

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ne dai ya jagoranci zaman maajalisar zartarwa na wannan mako sakamakon ziyarar da shugaba Buhari ya kai jihar Borno, sannan daga nan ya garzaya kasar Birtaniya.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugabar ma’aikatan tarayya, Wanifred Oyo-Ita da ministoci 20 ne suka hallara, yayinda aka dakatar da manema labarai daga shiga zauren, ministocin tarayya 31 a majalisar, bayan barin biyar daga cikinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel