Rashin tsaro: Arewa na cikin yaki – Marafa

Rashin tsaro: Arewa na cikin yaki – Marafa

- Sanata Kabiru Marafa ya koka kan halin rashin tsaro a Arewa

- Dan majalisan yace ana yaki a Arewa sannan yace lallai abubuwa za su iya tabarbarewa idan ba a yi wani abu ba a kai

- Marafa ya gargadi shugabannin arewa da kada suyi tunanin za su iya samun mafaka a Abuja, cewa yana iya zuwa ya komo

Sanata mai wakilan Zamfara ta tsakiya a majalisar dokokin kasa, Kabiru Marafa, ya koka kan halin rashin tsaro a yankin Arewa.

A cewar Sahara Reporters, dan majalisar, da yake magana a zauren majalisa ya bayyana cewa Arewa na cikin yaki.

Rashin tsaro: Arewa na cikin yaki – Marafa

Rashin tsaro: Arewa na cikin yaki – Marafa
Source: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Marafa yace kada wanda ya shiga rudu akan gaskiyar halin da Arewa ke ciki, inda yace lallai idan ba a yi wani abu ba, lamarin zai iya tabarbarewa.

Marafa ya gargadi shugabannin arewa da kada suyi tunanin za su iya samun mafaka a Abuja, cewa yana iya zuwa ya komo.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Alhamis ne gwamna mai hawa biyu a jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya bayyana cewar Najeriya ba addu'a take bukata ba, duk da kasancewar yin addu'a na da muhimmanci.

Dankwambo, tsohon babban akawun gwamnatin tarayya kafin a zabe shi a matsayin gwamna, a karo na farko, a shekarar 2011, ya ce shugabannin nagari Najeriya ke bukata ba addu'a ba.

"Ya na da kyau a yi addu'a amma Najeriya ba addu'a take bukata ba. Abinda muke bukata shine shugabanni nagari, hazikai," a cewar gwamnan.

Sai dai wannan mataki na gwamna Dankwambo ya saba wa fahimtar wasu daga cikin 'yan siyasa da malaman addini da suka dade suna kiran ake yiwa Najeriya addu'a domin ta samu hawa tudun tsira.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel