Kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli ta kori dilibai 60 saboda magudin jarabawa

Kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli ta kori dilibai 60 saboda magudin jarabawa

-Hukumar makarantar kere-kere da fasaha ta Nuhu Bamalli ta sallami dalibai 60

-Korar wadannan dalibai dai ya kasance ne a dalilin tafka magudi da aringizo yayin rubuta jarabawa a kakar karatun 2017/2018

Hukumar makarantar Nuhu Bamalli dake Zaria jihar Kaduna ta shaida korar dalibai 60 a dalilin magudin jarabawa tun kakar karatu na 2017/2018. Yan jarida sun ruwaito cewa an kori wadannan daliban ne cikin zango na farko da kuma na biyu na kakar karatun 2017/2018.

Shugaban makarantar, Dr Muhammad Kabir Abdullahi shine yayi wannan bayani a ranar Alhamis wurin bikin rantsar da sabbin dalibai 5,813 na kakar karatun 2018/2019.

Kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli ta kori dilibai 60 saboda magudin jarabawa

Kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli ta kori dilibai 60 saboda magudin jarabawa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Addu'a na da muhimmanci, amma ba ita Najeriya ke bukata ba - Dankwambo

Shugaban ya fayyace mana cewa cikin mutane 15,114 da suka samu guraben karatu a kwalejin, mutum 5,813 ne kawai suka yi rejista kawo ga ranar 24 ga watan Afrilu da aka kulle rejistar.

Bugu da kari, Kabiru ya ja hankanlin sabbin daliban da su guji tafka kowane irin magudi yayin da ake jarabawa. Hada da duk wani abinda ya sabawa dokar makarantar domin samun ilimi mai amfani sanin cewa abinda ya kawosu makarantar kenan.

Ya kara da cewa, kwalejin an budeta ne shekara 30 baya a matsayin Kwalejin fasaha da kere-kere ta Kaduna yayinda aka sauya mata suna daga baya zuwa marigayi Magajin Garin Zazzau Mallam Nuhu Bamalli.

Haka zalika, tun bude wannan makaranta , ta samu kyakkyawan jagoranci daga wurin tsofaffin shuwagabanninta guda 5 wadanda suka hada da: marigayi Alhaji Aliyu Muhammad Shika, Mallam Suleiman Aliyu, Alhaji Adamu Aliyu Shika, Farfesa Dalhatu Yahaya da kuma Farfesa Shehu Dalhatu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel