Addu'a na da muhimmanci, amma ba ita Najeriya ke bukata ba - Dankwambo

Addu'a na da muhimmanci, amma ba ita Najeriya ke bukata ba - Dankwambo

Da yammacin ranar Alhamis ne gwamna mai hawa biyu a jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya bayyana cewar Najeriya ba addu'a take bukata ba, duk da kasancewar yin addu'a na da muhimmanci.

Dankwambo, tsohon babban akawun gwamnatin tarayya kafin a zabe shi a matsayin gwamna, a karo na farko, a shekarar 2011, ya ce shugabannin nagari Najeriya ke bukata ba addu'a ba.

"Ya na da kyau a yi addu'a amma Najeriya ba addu'a take bukata ba. Abinda muke bukata shine shugabanni nagari, hazikai," a cewar gwamnan.

Sai dai wannan mataki na gwamna Dankwambo ya saba wa fahimtar wasu daga cikin 'yan siyasa da malaman addini da suka dade suna kiran ake yiwa Najeriya addu'a domin ta samu hawa tudun tsira.

Addu'a na da muhimmanci, amma ba ita Najeriya ke bukata ba - Dankwambo

Ibrahim Hassan Dankwambo; gwamnan jihar Gombe
Source: Depositphotos

Alal misali, a watan Fabrairu na shekarar 2019, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa na bukatar addu'a domin ta samu nasarar rubanya kokarinta da cigaba da yaki da cin hanci.

Shugaban kasar ya yi wannan furuci ne lokacin da yake gabatar da jawabi ga sarakunan gargajiya a gidan gwamnatin jihar Jigawa dake Dutse. Buhari ya kara da cewa saboda yakin da ya yi da cin hanci a lokacin da yake mulki a matsayin soja, aka yi masa juyin mulki tare da kulle shi a kurkuku na tsawon shekara uku.

DUBA WANNAN: Jami'an KASTELEA sun kashe mutum guda, sun raunata wani a Zaria

A lokuta dama, malaman addinin Islama da na Kirista sun sha yin kira tare da shirya taro na musamman domin gudanar da addu'a ga Najeriya.

Tun kafin wannan kalami na gwamna Dankwambo, akwai 'yan Najeriya da dama dake da ra'ayin cewar ba addu'a Najeriya keda bukata ba, su kan bayyana cewar matukar ba a gyara salon shugabanci da yadda ake gudanar da harkokin gwamnati ba, addu'ar ma ba za tayi tasiri ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel