John Mahama, Oyegun, Otedola da Kachikwu zasu karbi lambar girma na Zik 2018

John Mahama, Oyegun, Otedola da Kachikwu zasu karbi lambar girma na Zik 2018

-Wasu shahararrun mutane a Afrika sun samu kambar yabo

-Zik award zata karrama wasu manyan mutane bisa ga taka rawar gani a fannin ayyukansu

Tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama, John Odigie Oyegun, Ibe Kachikwu da Femi Otedola suna daga cikin manyan mutanen da za’a karrama da lambar girma ta Zik 2018.

Yayinda yake bayyana sunayen wadanda suka samu lambar girman ga yan jarida, sakataren kwamitin bada wannan kyauta Farfesa Pat Utomi yace, an fara bada wannan kyautane a shekarar 1995 domin tunawa da marigayi Nnamdi Azikwe kana kuma a habbaka shugabanci a fadin Afrika.

John Mahama, Oyegun, Otedola da Kachikwu zasu karbi lambar girma na Zik 2018

John Mahama, Oyegun, Otedola da Kachikwu zasu karbi lambar girma na Zik 2018
Source: UGC

DUBA WANNAN:Majalisar dattijai ta ki amincewa da Kogi a matsayin jihar dake da man fetur

Akwai jerin gwanon mutane da dama wanda aka fitar kafin zaben gwani a kowane mataki da muke dashi.

“ An tsara bikin wannan shekara ne ta yanda zai kasance daidai da al’adunmu wadanda muke tinkaho dasu a yankin Afrika.”

A matakin shugabanni John Mahama ne da John Odigie Oyegun wanda shine tsohon shugaban jam’iyar APC na kasa suka samu nasara.

Yayinda a matakin yan kasuwa kuwa, Femi Otedola da Arthur Eze sune sukayi nasara. Har wa yau a matakin kyakkyawan jagoranci kuwa akwai Udom Emmanuel da Sanni Bello sune suka yi nasarar lashe wannan kyauta.

Sauran mutanen da zasu karbi lambar girma a wannan wurin sun hada da: Shyngle Wigwe, Ibe Kachikwu, Oye Ibidapo-Obe, Philips Oduoza da kuma uwargidan gwamnan Ekiti Bisi Adeleye Fayemi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel