Jonathan ya haramtawa tsohon hadimin sa sukar Buhari

Jonathan ya haramtawa tsohon hadimin sa sukar Buhari

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya umurci tsohon hadimin sa Reno Omokri, a kan ya rika girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda hadimin ya bayar da shaida a shafin sa na sada zumunta.

Ko shakka ba bu kasashen duniya na ci gaba da karrama tsohon shugaban kasa Jonathan a sakamakon hali na tawakkali da daukan dangana da ya nuna yayin da shugaban kasa Buhari ya lallasa shi a babban zaben kasa na 2015.

Sai dai tsohon hadimin Jonathan bai gushe ba yana ci gaba da suka da kuma caccakar shugaban kasa Buhari tare da akidu gami da tsare-tsaren gwamnatin sa wajen riko da akalar jagorancin kasar nan.

Jonathan ya haramtawa tsohon hadimin sa sukar Buhari

Jonathan ya haramtawa tsohon hadimin sa sukar Buhari
Source: UGC

Mista Omokri ya sake jaddada hali na dattako da karamci da Mai Duka ya azurta tsohon Ubangidan sa da a cewar sa zuciyar sa ta tsarkaka daga tsananin adawa na siyasa. Ya hikaito yadda ya kiraye shi domin tsawatar da shi a kan haramcin caccakar shugaban kasa Buhari.

Omokri ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Jonathan ya shawarce shi a kan girmama shugaban kasa Buhari da a cewar ba bu wani tsohon shugaban kasa da mai makamanciyar wannan kyakkyawar dabi'a.

KARANTA KUMA: Dalibai 19 sun kashe kansu bayan faduwa jarrabawa a kasar India

Ya buga misali da cewa tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida da kuma takwaran sa, Cif Olusegun Obasanjo ba za su taba hawa bisa makamancin wannan sahu na dattako mai aminci da mai Mai Duka ya azurta Ubangidan sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel