Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi, hotuna

Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi, hotuna

Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, Ali Aji Janga, ya kaddamar da atisayen 'Puff Adder'.

A kalla masu laifi 39 rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta kama yayin kaddamar da atisayen na 'Puff Adder' domin dakile aiyukan laifi da jihar ke fama da su.

Da yake gabatar da jawabi a wurin kaddamar da atisayen, Janga ya bayyana cewar rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen ne domin yin biyayya ga babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Abubakar.

Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi, hotuna

Ali Aji Janga yayin gabatar da jawabi

Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi, hotuna

Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi

Rundunar 'yan sanda ta kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi, hotuna

Jami'an rundunar 'yan sanda yayin kaddamar da atisayen 'Puff Adder' a Bauchi
Source: Twitter

Janga ya bayyana hakan ne a hedikwatar rundunar 'yan sandan jihar Bauchi da ke kan titin Yandoka yayin da ayke gabatar da masu laifin su 39 da suka hada da masu masu satar mutane da 'yan fashi da mukami.

IGP Abubakar ne ya fara kaddamar da atisayen 'Puff Adder' domin kawo karshen kalubalen tsaro a sassan kasar nan, musamman matsalar garkuwa da mutane a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna da sauran sassan kasa.

Daga cikin makaman da aka samu a tare da masu laifin akwai bindigar baushe 5, adda guda 9, sharbebiyar wuka 1, babura uku da kuma ganyen tabar wiwi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel