Dalibai 19 sun kashe kansu bayan faduwa jarrabawa a kasar India

Dalibai 19 sun kashe kansu bayan faduwa jarrabawa a kasar India

A garin Telanga na kasar Indiya, kimanin dalibai 19 sun katswewa kawunan su hanzari bayan faduwa jarrabawar ajin karshe kamar yadda rahotanni da hukumomi a kasar suka bayyana a ranar Alhamis.

Dalibai 19 sun kashe kansu bayan faduwa jarrabawa a kasar India

Dalibai 19 sun kashe kansu bayan faduwa jarrabawa a kasar India
Source: Depositphotos

Iyaye da dalibai da dama ba su gushe ba wajen ci gaba da gudanar da zanga-zanga afdin jihar Telanga tun yayin da marantar ta fidda sakamakon jarrabawar daliban ta a ranar Alhamis 18 ga watan Afrilun 2019.

Cikin kimanin dalibai 974,00 da su ka zana jarrabawar a bana, dalibai 328,000 sun yi rashin sa'a yayin da su ka fadi jarrabawar kamar yadda Ministan jihar, Chandrasekhar ya bayyana cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai.

Sai dai a yayin da ya kafa wani kwamitin amintattu na mutum uku domin gudanar da bincike kan yadda hukumar makarantar ta gudanar da jarrabawar, tuni dalibai 19 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon rashin tawakkali na riko da kaddarar da ta auku a kansu.

KARANTA KUMA: Gwamna Yari ya amince da N30,000 mafi karancin albashin ma'aikatan jihar Zamfara

A yayin da hukumar makarantar ta yanke shawarar sake gudanar da dogon nazari na jin kai a kan sakamakon jarrabawar, tuni dai rayukan dalibai da suka salwantar da kawunan su a sakamakon bakin ciki sun kai kimanin 19 kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel