Buhari ya tashi zuwa Ingila daga Maiduguri (Bidiyo)

Buhari ya tashi zuwa Ingila daga Maiduguri (Bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala ziyarar aiki a jihar Borno, sannan ya tashi zuwa birnin Landan na kasar Ingila daga filin jirgin saman Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Buhari ya tashi ne a jirgin shugaban kasa. Ana sa ran zai dawo gida Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu, 2019.

Tun a kwanakin baya kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewar shugaba Buhari zai tafi hutu zuwa kasar Ingila bayan kammala ziyarar aiki a jihar Borno a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu.

Buhari ya tashi zuwa Ingila daga Maiduguri (Bidiyo)

Buhari ya tashi zuwa Ingila
Source: Twitter

Ana saka ran shugaba Buhari zai dawo Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu, kwanaki 17 zuwa ranar da zai rushe dukkan mukaman siyasar da ya nada.

DUBA WANNAN: A karshe: Hukumar AIB ta saki rahoton dalilin faduwar jirgin tsohon gwamna Suntai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rushe dukkan masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa a ranar 22 ga watan Mayu bayan ya jagoranci zaman majalisar zartar wa ta tarayya (FEC) a ranar, kamar yadda ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya sanar.

Mohammed ya sanar da haka ne a ranar Alhamis yayin da yake magana da manema labarai bayan kammala taron FEC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel