Gwamna Yari ya amince da N30,000 mafi karancin albashin ma'aikatan jihar Zamfara

Gwamna Yari ya amince da N30,000 mafi karancin albashin ma'aikatan jihar Zamfara

Gwamnan Abdulaziz Yari Abubakar na jihar Zamfara, ya yi amanna da sabon kudirin N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan jihar sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamisa 18 ga watan Afrilu, ya shigar da N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan cikin doka

Gwamna Yari ya sha alwashin sauke nauin bashin 'yan fansho gabanin barin kujerar sa a ranar 29 ga watan Mayu.

Gwamna Abdulaziz Yari Abubakar na jihar Zamfara, ya amince da Naira dubu talatin a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan jihar sa yayin da gwamnatin tarayya ta shigar da kudirin cikin dokar kasa a kwana-kwanan.

Gwamna Yari tare da shugaban kasa Buhari

Gwamna Yari tare da shugaban kasa Buhari
Source: UGC

Wakilin mu na reshen jihar Zamfara, Lawal Tsalta, ya ruwaito cewa gwamna Yari ya yi amanna da wannan sabon kudiri na mafi karancin albashin ma'aikata a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilun 2019 yayin halartar taron kungiyar kwadago reshen jihar da aka gudanar karo na shida.

Gwamna Yari ya bayyana cewa magajin kujerar sa zai tabbatar da wannan sabon kudiri na mafi karancin albashin ma'aikata cikin inganci ko da kuwa bai samu damar aiwatar wa ba gabanin barin kujerar sa ta jagoranci a jihar.

Ya kuma alwashin sauke nauyin dukkanin bashin masu karbar fansho gabanin barin kujerar sa ranar 29 ga watan Mayun 2019.

KARANTA KUMA: Ka da a yi jinkiri wajen nadin Ministoci - Jigon APC ya shawarci Buhari

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, gwamnan jihar Anambra Willie Obiano, ya ce tabbatar da N30,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikatan jihar sa zai kara fiye da Naira biliyan biyu kan nauyin albashi da zai rataya a wuya gwamnatin sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel