A karshe: Hukumar AIB ta saki rahoton dalilin faduwar jirgin tsohon gwamna Suntai

A karshe: Hukumar AIB ta saki rahoton dalilin faduwar jirgin tsohon gwamna Suntai

Hukumar binciken hatsari ta kasa (AIB) ta saki rahotannin wasu binciken hatsarin jirgin sama guda hudu tare da bayar da wsu shawarwari guda 24.

Daga rahotannin da AIB ta saki akwai na hatsarin da ya ritsa da jirgin Cessna 208B da tsohon gwamnan jihar Taraba, Danbaba Sunati, ke tuka wa, wanda ya fadi a daf da filin saukar jirage na Yola a ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2012.

Da yake jawabi a kan rahoton sakamakon binciken, kwamishina a hukumar AIB, Injiniya Akin Olateru, ya ce binciken da suka gudanar a kan hatsarin da ritsa da tsohon gwamnan ya nuna cewar marigayin bashi da kware wa ko cikakken horon tuka jirgin sama.

A karshe: Hukumar AIB ta saki rahoton dalilin faduwar jirgin tsohon gwamna Suntai

Marigayi Danbaba Danfulani Suntai
Source: Twitter

Duk da ya tsira da ran sa bayan hatsarin, an cigaba da jigilar asibiti da tsohon gwamna domin nema masa lafiya kafin daga bisani ya mutu a shekarar 2017.

A cewar shugaban AIB, duk da tsohon gwamnan na da direbansa mai lasisi, ya zabi ya ke tuka jirgin da kan sa duk da bai samu takardar sahalewar hukumar kula da jiragen sama ta kasa (NCAA) ba.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa

Bayan hakan, an gano cewar bai samu shaida daga kowacce irin hukuma da ke sahale wa mutum tuka jirgin sama ba bayan an bashi horo.

Kwamishinan ya bayyana cewar hatta jirgin marigayin bashi da rijista da kowacce hukumar kamfanonin jiragen sama ko kuma wata hukuma da ke duba lafiyar jiragen sama.

Ya yi kira ga hukumar NCAA da ta kara mayar da hankalin a kan aikinta na kula da duk wani jirgi da ke tashi zuwa sararin samaniya a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel