Ku daina barin kananan yara da jarirrai a gaban talabijin, shawara daga kungiyar lafiya ta duniya (WHO)

Ku daina barin kananan yara da jarirrai a gaban talabijin, shawara daga kungiyar lafiya ta duniya (WHO)

-Yara yan kasa da shekara 2 basu da bukatar zama gaban talabijin domin yin kallo

-Komai yayi yawa kan iya zama matsala, zama gaban talabijin musamman ga kananan yara ya haifar da matsaloli iri daban-daban

Kananan yara yan kasa da shekara 2 da haihuwa bai kamata ace ana barinsu gaban talabijin ba, Wannan wata sabuwar ka’idane da ta fito daga bakin kungiyar lafiya ta duniya.

Abinda yafi da cewa da yaran suyi shine karatu ko kuma mai lura da su ya basu labari, ko da na awa guda ne. Har wa yau, yara masu shekara 2 zuwa 4 zasu iya yin kallon na awa daya kacal shima din ba a ko da yaushe ba.

Ku bar barin kananan yara da jarirrai a gaban talabijin, shawara daga kungiyar lafiya ta duniya (WHO)

Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus
Source: UGC

KU KARANTA:Da duminsa: Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa

Bugu da kari, zama na tsawon lokaci gaban talabijin kan iya haifarwa wadannan yara da rashin lafiya. Yawan zaman da yara keyi gaban talabijin kan haifar da matsalar kiba da ya wuce kima a turance ‘Obesity’.

“ Yarinta wani lokacine da yaro kan iya daukan duk abinda ya taso a kai a matsayin dabi’a wacce zata iya bin shi har girmanshi”. A fadar shugaban kungiyar lafiya ta duniya Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus. Domin haka abu mafi kyau shine a gina yaran kan hanyar da zata inganta lafiyarsu ba wacce zata zame masu matsala ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel