Garkuwa da Mutane: Majalisar Dattawa ta gayyaci Sufeton 'Yan sanda

Garkuwa da Mutane: Majalisar Dattawa ta gayyaci Sufeton 'Yan sanda

Majalisar dattawan Najeriya ta nemi sufeto janar na 'yan sanda Muhammadu Adamu, da ya bayyana gaban ta domin jin ta bakin sa dangane da yadda ta'addanci masu garkuwa da Mutane ke ci gaba da kamari a fadin kasar nan.

Majalisar sanatocin Najeariya ta ce ta gayyaci jagoran na hukumar 'yan sanda domin samun masaniya tare da kulla dabaru da shawarwari na kawo karshen annobar ta'addancin garkuwa da mutane a kasar.

Sufeto Janar na 'Yan sanda; Muhammadu Adamu

Sufeto Janar na 'Yan sanda; Muhammadu Adamu
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar ta yanke shawarar gayyatar babban jami'in na hukumar 'yan sanda biyo bayan kudiri da wakilin shiyyar Kaduna da Tsakiya ya gabatar, Sanata Shehu Sani.

Bayan tattaunawa a kan batutuwan ta'addancin masu garkuwa da mutane musamman yadda su ke cin karen su ba bu babbaka a yankunan jihar Kaduna, majalisar ta yanke shawarar gayyatar sufton na 'yan sanda domin tumke damarar dasa aya kan wannan mummunan kalubale.

KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Dole hukumomin tsaro su hada kai domin yakar ta'addanci a Najeriya - Bichi

Yayin tafka muhawara a zauren majalisa, Sanata Sani ya ce ta'addancin masu garkuwa da kashe-kashen al'umma baya ga kone gidaje a wasu kauyukan jihar Kaduna ya kai intaha da kawo yanzu an gazo gano bakin zaren.

Da ya ke ci gaba da jaddada yadda ta'addanci ya yi kamari, Sanatan Shehu ya ce a halin yanzu yankunan Kajuru da kuma jihar Kaduna baki daya ta zamto wani dandali a yankin Arewacin Najeriya da ake cin kasuwar kashe-kashe da ta'addancin garkuwa da Mutane.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel