Da duminsa: Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa

Da duminsa: Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa

- Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce shugaba Buhari zai rushe dukkan mukaman siyasar da ya nada a ranar 22 ga watan Mayu

- Shugaba Buhari zai sauke masu rike da mukaman siyasar ne bayan ya dawo daga hutun da zai yi a kasar Ingila

- Tun a kawanakin baya Femi Adesina, kakakin shugaban kasa, ya bayyana cewar shugaba Buhari zai wuce kasar Ingila daga Maiduguri, jihar Borno

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai rushe dukkan masu rike da mukaman siyasa a gwamnatinsa a ranar 22 ga watan Mayu bayan ya jagoranci zaman majalisar zartar wa ta tarayya (FEC) a ranar, kamar yadda ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya sanar.

Mohammed ya sanar da haka ne a ranar Alhamis yayin da yake magana da manema labarai bayan kammala taron FEC.

Da duminsa: Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa

Buhari ya saka ranar sallamar dukkan ministoci da hadiman sa
Source: Facebook

Tun a kwanakin baya kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewar shugaba Buhari zai tafi hutu zuwa kasar Ingila bayan kammala ziyarar aiki a jihar Borno a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu.

DUBA WANNAN: Ministar kudi ta fadi dalilin da yasa gwamnati ba ta iya kaddamar da kasafin kudi a shekara

Ana saka ran shugaba Buhari zai dawo Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu, kwanaki 17 zuwa ranar da zai rushe dukkan mukaman siyasar da ya nada.

A shekarar, 2017, Buhari ya shafe kwanaki 103 yana zaman jinya a kasar Ingila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel