Rashin Tsaro: Dole hukumomin tsaro su hada kai domin yakar ta'addanci a Najeriya - Bichi

Rashin Tsaro: Dole hukumomin tsaro su hada kai domin yakar ta'addanci a Najeriya - Bichi

Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Yusuf Bichi, ya ce tabbatar da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro ita kadai ce hanya mafi dace wajen tunkara tare da kawo karshen annobar ta'addanci a fadin kasar nan.

Ya jaddada cewa dole hukumomin tsaro na Najeriya su hada gwiwa da juna wajen fuskantar kalubale na rashin tsaro musamman ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe a wasu sassan kasar nan.

Yusuf Bichi tare da shugaban kasa Buhari
Yusuf Bichi tare da shugaban kasa Buhari
Source: Twitter

Kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito, shugaban hukumar na DSS ya ce wannan tsari na hadin gwiwa tsakanin dukkanin hukumomin tsaro ya kasance mafi kyautatuwar sabuwar akida ta tabbatar da bunkasar harkokin tsaro a fadin duniya.

Bichi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa yayin taron ku ngiyar kakakin hukumomin tsaro na Najeriya da aka gudanar a hedikwatar hukumar DSS da ke garin Abuja a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu.

Ya yi kira na neman hukumomin tsaro da su yi bajakolin arzikin kwarewar su domin tallafawa juna wajen inganta harkokin tsaro a Najeriya.

KARANTA KUMA: Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a Dajin Sambisa

Jagoran hukumar ya hikaito iren-iren kalubale na rashin tsaro da ya kamata kasar nan ta tsarkaka da su cikin gaggawa da suka hadar garkuwa da mutane, satar shanu, rikicin makiyaya da manoma, fatauci muggan kwayoyi da kuma sauran ababe na kyama.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel