Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a Dajin Sambisa

Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a Dajin Sambisa

Rundunar dakarun saman sojin Najeriya mai fafutikar tabbatar da zaman lafiya wajen yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ta samu nasarar kai wani hari na luguden a kan sansanin 'yan Boko Haram cikin Dajin Sambisa.

Rundunar sojin mai lakabin gudanarwa ta Operation Lafiya Dole, ta samu nasarar yiwa 'yan kungiyar masu tayara da kayar baya na Boko Haram luguden wuta tare da Motocin su cikin wani sansani a dajin Sambisa da ke Arewa maso Gabashin kasar nan.

Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a Dajin Sambisa

Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a Dajin Sambisa
Source: Twitter

Bayan daukar lokaci wajen gudanar da sintiri da kai komo na leken asiri, rundunar sojin a ranar Larabar da ta gabata hakar ta ta cimma ruwa yayin da ta samu nasarar yiwa masu mummunar ta'ada shigar bazata a sansanin su kamar yadda kakakin rundunar sojin sama na kasa ya bayyana, Air Commodore Ibikunle Daramola.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rundunar sojin yayin amfani da jiragen ta na yaki ba ta sassautawa 'yan Boko Haram ba yayin da su ka yi yunkurin tserewa inda gabanin su kai ga mafaka harshen wuta ya babbake su kurmus.

KARANTA KUMA: Ku taimaka mana wajen yakar ta'addancin Boko Haram - Najeriya ta roki kasar Rasha

A halin yanzu rundunar dakarun tsaro tare da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na ci gaba da ikirarin dakusar da kaifin ta'addanci na kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Dubi Bidiyon luguden wuta da rundunar sojin sama ta yiwa 'yan ta'adda na Boko Haram a dajin Sambisa

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel