Gwamnati za ta biya kaakakin majalisa N500,000 duk wata a matsayin fansho

Gwamnati za ta biya kaakakin majalisa N500,000 duk wata a matsayin fansho

Masu mulki na shagalinsu, su kadai ke watanda da kudaden al’umma yadda suka ga dama, anan majalisar dokokin jahar Bayelsa ce ta amince da biyan makudan kudade ga yayanta a matsayin kudin fansho na dindindin bayan sun bar majalisar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan majalisa Peter Akpe ne ya gabatar da kudurin a gaban majalisar tunda fari, kudurin daya tanadi biyan Kaakakin majalisa naira dubu dari biyar (N500,000) a duk wata a matsayin kudin fanshonsa bayan ya bar majalisa.

KU KARANTA: Kungiyar kwadago ta dauki alwashin tursasa gwamnoni biyan karancin albashin N30,000

Gwamnati za ta biya kaakakin majalisa N500,000 duk wata a matsayin fansho

Majalisar dokokin Bayelsa
Source: UGC

Haka zalika kudurin dokar ta tanadi gwamnati ta biya mataimakin kaakakin majalisa naira dubu dari biya (N200,000) a duk wata a matsayin nasa kudin fanshon, yayin da dokar ta nemi a biya sauran karabitin yan majalisa naira dubu dari dari (N100,000) duk wata.

Bugu da kari dokar ta sanya tsofaffin yan majalisun dokokin jahar a cikin wadanda zasu ci gajiyar wannan tagomashi, kai hatta yan majalisa yan asalin jahar Bayelsa da suka wakilci jama’ansu a tsohuwar majalisar jahar Ribas kafin samar da jahar Bayelsa zasu mori waannan sabon tsarin fansho.

A yanzu haka dai ana tsimayin gwamnan jahar Bayelsa Seriake Dickson ya rattafa hannu akan wannan kudurin doka kafin ta zama doka har ta fara aiki, sai dai jama’an jahar Bayelsa da dama sun nuna bacin ransu game da wannan kudurin doka.

Wani dan asalin Bayelsa, Fidel Boboye ya bayyana dokar a matsayin muguwar doka dake nuna tsananin yunwar shuwagabannin siyasa, yayi mamakin yadda za’ace gwamnati na kara ma mai karfi karfi duk da tarin dukiyar da yan majalisan suke dashi.

Shi kuma wani mai suna Preye Alegbe cewa yayi “Wannan bai yi yawa ba kuwa, duba da cewa akwai dimbin matasa da suka kammala karatu amma basu da aikin yi? Mai yasa ba zasu saka kudaden a cikin tsarin da zasu amfani matasa ba?”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel