Kungiyar kwadago ta dauki alwashin tursasa gwamnoni biyan karancin albashin N30,000

Kungiyar kwadago ta dauki alwashin tursasa gwamnoni biyan karancin albashin N30,000

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta dauki alwashin sanya duk gwamnonin Najeriya a gaba don har sai sun biya naira dubu talatin a matsayin karancin albashin ma’aikata, hakanan zasu saka kafar wando daya da duk gwamnan daya gaza biyan albashin.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 24 ga watab Afrilu yayin da yake kaddamar da wani katafaren gidan yan fansho a garin Ibadan na jahar Oyo, inda ya bayyana shuwagabannin gwamnati a matsayin makiyan ma’aikata.

KU KARANTA: Gwamnatin Saudiyya zata gina matatar mai ta zamani a Najeriya

Ayuba Wabba wanda ya samu wakilcin shugaban kungiyar kwadago ta jahar Oyo, Waheed Olojede ya kaddamar da gidan yan fanshon ne dake dauke da dakin taro mai cin mutane dubu daya, gidan rediyo, karamin asibiti don kulawa da yan fansho da kuma cibiyar kimiyya da fasaha.

“Mun gode ma Allah daya kawomu karshen gwagwarmayar karin albashi wanda muka fara tun a shekarar 2011 har zuwa ranar Alhamis da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa hannu akan dokar, wanda hakan yasa dole ne duk wani mai daukan aiki ya biya ma’aikatansa N30,000 a matsayin karancin albashi.

“Sai dai abin haushin shine shuwagabannin gwamnatoci a kowanni mataki makiyan ma’aikata ne, ba kasafai suka fiya son bin umarnin dokar dake kula da walwalar ma’aikata ba, amma tunda har mun samu nasarar N30,000 zamu tabbata kowanni gwamna ya biya” Inji shi.

Daga karshe Wabba yace tare da kungiyar gwamnonin Najeriya aka cimma wannan sabon dokar karancin albashin, don haka ba zasu sassauta wajen gwagwarmayar ganin sun sauke nauyin dake rataye a wuyansu ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel