Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa inda ministoci 20 suka hallara

Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa inda ministoci 20 suka hallara

A yanzu haka mataimakin Shugaban kasa,Yemi Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zartarwa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya jagoranci zaman a makon da ya gabata ya tafi jihar Borno. Sannan daga bisani zai tafi kasar Birtaniya ziyarar sa kai.

An rahoto cewa, an fara taron ne bayan isowar mataimakin Shugaban kasa zauren majalisar da ke fadar Shugaban kasa da misalin karfe 11:01am.

Babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugabar ma’aikatan tarayya, Wanifred Oyo-Ita da ministoci 20 ne suka hallara, yayinda aka dakatar da manema labarai daga shiga zauren, ministocin tarayya 31 a majalisar, bayan barin biyar daga cikinsu.

Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa inda ministoci 20 suka hallara

Yanzu Yanzu: Mataimakin Shugaban kasa, Osinbajo ya jagoranci zaman majalisa inda ministoci 20 suka hallara
Source: Depositphotos

A karshen ganawar, ministoci za su sanar da manema labarai na fadar Shugaban kasa sakamakon ganawar.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya kaddamar da sabon katafaren ginin makaranta a hedikwatar soji a Jaji (Hotuna)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu bayan ya ziyarci Maiduguri, jihar Borno, ofishin labaransa ta bayyana.

A ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu ne Shugaban kasar ya ziyarci Lagas inda ya kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel