Hukumar soji ta bukaci mazauna yankin kudu maso gabas da kada su tsorata da shige da fice sojoji

Hukumar soji ta bukaci mazauna yankin kudu maso gabas da kada su tsorata da shige da fice sojoji

Hukumar sojojin Najeriya ta bukaci mazauna yankin kudu maso gabas da kada su daga hankali akan shige da ficen dakarunta da kuma karan harbe-harbe yayinda suke gudanar da wani shirinsu na shekara na 2019.

Mataimakin daraktan kakakin rundunar sashi na 82, Kanal Aliyu Yusuf, ya yi rokon a wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu a Enugu.

Yusuf ya bayyana cewa shige da ficen sojojin a yankin da kuma karan harbe-harben zai afku ne a lokacin shirin.

Hukumar soji ta bukaci mazauna yankin kudu maso gabas da kada su tsorata da shige da fice sojoji

Hukumar soji ta bukaci mazauna yankin kudu maso gabas da kada su tsorata da shige da fice sojoji
Source: Depositphotos

A cewarsa, don haka ana bukatar jama’a dasu ci gaba da gudanar da harkokin gabansu ba tare da tsoro ba domin wannan shiri ne da sojoji suka saba.

KU KARANTA KUMA: Zan kawo karshen gabar da ke tsakanin Saraki da Tinubu – Kalu

A wani lamari na daban, mun ji cewa Shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar TY Buratai, ya bude sabon katafaren ginin makarantar sojojin 'infantry' da aka yi a cikin hedikwatar soji ta Jaji da ke jihar Kaduna.

Buratai da ragwar manyan hafsoshin rundunar sojin kasa na jihar Kaduna domin halartar wani muhimmin taro da za a yi a cikin satin nan.

Kafin ya wuce zuwa Jaji domin kaddamar da sabon ginin na zamani, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar tawagar shugabannin rundunar soji a karkashin jagorancin shugaban rundunar soji ta kasa, Laftanal Janar TY Buratai, sun ziyarci fadar gwamnatin jihar Kaduna da safiyar ranar Laraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel