Ku taimaka mana wajen yakar ta'addancin Boko Haram - Najeriya ta roki kasar Rasha

Ku taimaka mana wajen yakar ta'addancin Boko Haram - Najeriya ta roki kasar Rasha

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi agajin kasar Rasha wajen kawo karshen ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram musamman a Arewa maso Gabashin kasar nan da kuma gabar tafkin Chadi.

Gwamnatin tarayya da sanadin Ministan tsaro na kasa, Mansur Dan Ali, ya mika kokon bara yayin halartar taron tsaro na duniya karo na takwas da aka gudanar cikin birnin Moscow na kasar Rasha a ranar Larabar da ta gabata.

Ministan Tsaro; Mansur Dan Ali

Ministan Tsaro; Mansur Dan Ali
Source: UGC

Ministan Tsaro ya kuma nemi hadin gwiwar kasar Rasha wajen bayar da gudumuwar kariya ga yankunan teku na Najeriya da ke gabar tsuburin kasar Guinea.

Dan Ali yayin lura da kwarewar kasar Rasha wajen gudanar da harkoki na yakar ta'addanci cikin inganci, ya nemi kasar ta kawo dauki na kawo karshe tare da yaye annobar ta'addanci Boko Haram a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: Na yaba da kwazon aiki na gwamnan jihar Legas Ambode - Buhari

Ministan ya bayyana damuwa dangane da yadda ta'addanci ke ci gaba da tsanani nahiyyar Afirka inda ya buga misali musamman da kungiyoyi masu tayar da kayar baya na Boko Haram a kasashen da ke iyaka da tafkin Chadi, kungiyar Al-Shabaab mai cin karen ta ba bu babbaka a kasar Somalia da Kenya gami da kungiyar ISIS da ke tayar da zaune tsaye a kasar Mali.

Ya kuma yabawa gwamnatin kasar Rasha musamman ta bangaren tallafi da daukar nauyin karatun al'ummat Najeriya da tasirin hakan ke ciyar da kasar gaba tare da angiza ta zuwa tudun tsira.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel