Ka da a yi jinkiri wajen nadin Ministoci - Jigon APC ya shawarci Buhari

Ka da a yi jinkiri wajen nadin Ministoci - Jigon APC ya shawarci Buhari

Jagoran kungiyar yakin neman zaben kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC reshen jihar Ekiti, Dakta Olusegun Osinkolu, a aranar Larabar da ta gabata ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan gaggauta nadin Ministocin sa a sabuwar gwamnatin sa cikin wa'adin ta na biyu.

Osinkolu kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito ya bayyana cewa, rashin jinkiri wajen kafa majalisa zai taimaka kwarai da aniyya ta hanyar habaka inganci a yayin shimfidar tsare-tsare da akidu na gwamnati.

Ka da a yi jinkiri wajen nadin Ministoci - Jigon APC ya shawarci Buhari

Ka da a yi jinkiri wajen nadin Ministoci - Jigon APC ya shawarci Buhari
Source: UGC

Babban jigon na jam'iyya mai ci ta APC ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Larabar da ta gabata cikin birnin Ado Ekiti.

A yayin da shugaban kasa Buhari ya shafe tsawon watanni shida gabanin nadin Ministoci da kafa Majalisar sa cikin wa'adin gwamnatin sa na farko, jigon na APC ya ce maimacin makamancin wannan lamari a yanzu zai haifar da koma bayan wajen tafiyar da sabuwar gwamnatin sa cikin aminci.

KARANTA KUMA: Garkuwa da Mutane: Majalisar Dattawa ta gayyaci Sufeton 'Yan sanda

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Osinkolu bayan taya shugaban kasa Buhari murnar lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata, ya kuma yabawa shugaban kasardangane da bayar amincewar sa a kan sabon mafi karancin albashin ma'aikatan kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel