Kada ka tozarta shugabanninmu – Kungiyar matasan Arewa ga Tinubu

Kada ka tozarta shugabanninmu – Kungiyar matasan Arewa ga Tinubu

- Kungiyar matasan Arewa (AYCF) sun yi gargadi ga Asiwaju Bola Tinubu

- Kungiyar sun gargadi babban jigon jam’iyyar APC na kasa akan tozarta shugabannin arewa

- Sunce Tinubu da kudu maso yamma su gode ma Allah da irin dammar da suka samu a gwamnatin Buhari

Kungiyar matasan Arewa (AYCF) sun yi gargadi ga Asiwaju Bola Tinubu akan “tozarta” shugabannin yankin, musamman Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

A wajen taron gaggawa da suka kira a Kaduna a daren ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, kungiyar ta caccaki babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, a wani jawabi dauke da sa hannun shugabanta na kasa, Alhaji Yerima Shettima.

Kada ka tozarta shugabanninmu – Kungiyar matasan Arewa ga Tinubu

Kada ka tozarta shugabanninmu – Kungiyar matasan Arewa ga Tinubu
Source: Depositphotos

Kungiyar tace Tinubu da kudu maso yamma su gode ma Allah da dukkanin dammar da suka samu a gwamnatin Buhari, “musamman manyan mukamai masu gwabi-gwabi daga yankin kudu maso yamma da kuma daukar manyan ayyukan gwamnatin tarayya zuwa yankin kudu maso yamma.

“Ya kamata Cif Bola Tinubu ya sa a ransa cewa zamani ya wuce da wani dan siyasa daga kudu maso yamma zai wofantar da yan atewa. Ba abun yarda bane cewa Tinubu ya tozarta yayan arewa a bainar jamaá kamar Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai saboda muna alfahari dasu,” cewar sanarwar.

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta 9: Bana tunanin APC ta koyi darasi daga kuskurenta na 2015 - Sani

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Abia kuma zababben sanatan Abia ta arewa, Dr. Orji Uzor Kalu yayi alkawarin sasanta Shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki da babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Johannesburg, Kalu yayi alkawarin shiga tsakaninsu, inda ya bayyana cewa kada a bari siyasa ya haddasa rashin aminci a tsakanin yan uwa da abokan arziki.

Ya roki shugabannin biyu dasu janye takobinsu domin dorewar damokradiyyar kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel