Kungiyar NCA ta na goyon bayan Goje ya zama Shugaban Majalisa

Kungiyar NCA ta na goyon bayan Goje ya zama Shugaban Majalisa

Wata kungiya da ake kira North Central Alliance ta shirya tara mutane 2000 da za su fito su yi tattaki har zuwa gaban majalisar tarayya inda za su nuna goyon bayan su ga takarar Sanata Danjuma Goje.

Wannan kungiya ta na kokarin taya Sanata Mohammed Danjuma Goje kamfe ne a majalisar dattawa. Shugaban kungiyar ta North Central Alliance Kwamared Nasiru Isiyaku ya bayyanawa manema labarai wannan a Kaduna.

Kungiyar ta kuma yi kira ga sababbin Sanatocin APC da su zabi Danjuma Goje a matsayin shugaban majalisar dattawa, Nasiru Isiyaku, yake cewa Goje ya cancanci ya rike majalisar idan aka duba irin ayyukan da yayi wa APC.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai nemi shiga tsakanin Ndume, Goje da Lawan

Kungiyar NCA ta na goyon bayan Goje ya zama Shugaban Majalisa

Takarar Sanata Danjuma Goje a Majalisar Dattawa tana kara karfi
Source: Depositphotos

North Central Alliance take cewa Sanata Goje yayi wa mutanen Gombe namijin aiki a lokacin yana gwamna na tsawon shekaru 8 daga 2003 zuwa 2011, sannan kuma yana cikin manyan Sanatocin da ake ji da su a majalisar.

Danjuma Goje ya dace da tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari mai taken Next Level inji wannan kungiya don haka ta ke neman ‘ya ‘yan jam’iyyar da ke majalisa su mara masa baya wajen ganin ya gaji kujerar Bukola Saraki.

Kwamared Nasiru Isiyaku bai bayyana lokacin da kungiyarsa za ta shirya wannan tattaki ba, amma ya nuna cewa za su dura majalisa ne kafin lokacin zaben sabon shugaba. Isiyaku yayi wannan jawabi ne a Ranar 23 ga Afrilun nan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel