Ganduje ya bayyana wani bangare da zai bawa muhimmanci a mulkinshi karo na biyu

Ganduje ya bayyana wani bangare da zai bawa muhimmanci a mulkinshi karo na biyu

- Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce wannan gwamnatin tasa za ta bai wa bangaren ilimi muhimmanci fiye da komai

- Ya ce ya fuskanci cewa fannin ilimi ne ke kawo cigaba ga al'umma cikin gaggawa

- Ya bukaci iyayen yara da su goya masa baya wurin ganin ya cika burinshi na habaka fannin ilimin a jihar

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai bai wa bangaren ilimi muhimmanci matuka idan ya hau mulki a karo na biyu, ya nuna cewa lokacin zabe da cece-kuce na siyasa ya wuce, yanzu lokaci ne da ya kamata duka a hadu a hada karfi da karfe domin yin aiki da zai kawo cigaba ga jihar Kano.

Ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ba wa bangaren ilimi muhimmanci, saboda yanzu shine abinda ya fi kawo cigaba a cikin al'umma, zai tabbatar da cewa yara sun samu kayayyakin karatu masu kyau, don su zama kwararru a nan gaba.

Ganduje ya bayyana wani bangare da zai bawa muhimmanci a mulkinshi karo na biyu

Ganduje ya bayyana wani bangare da zai bawa muhimmanci a mulkinshi karo na biyu
Source: Depositphotos

A sanarwar da kwamishinan labarai da al'adu na jihar, Malam Muhammad Garba, ya ce daya daga cikin muhimman abubuwan da gwamnan jihar ya saka a gaba a wannan gwamnatin ta sa shine, bangaren ilimi, gwamnan ya ce zai sanya kudi sosai a bangaren ilimi domin kawo cigaba ga jihar baki daya.

Bayan haka kuma, ya nuna cewa gwamnati kadai ba za ta iya daukar nauyin karatun yaran ba,ya bukaci iyayen yaran su dinga sanyawa yara son yin karatu a zuciyarsu.

KU KARANTA: An kama mutanen da suka kashe 'yan sanda hudu da mata mai ciki

Kwamishinan ya ce gwamnatin kuma za ta mai da kai wurin kawo cigaba a bangaren ayyukan raya jiha, domin kawo cigaba a ciki da wajen jihar ta hanyar habaka tattalin arziki gina hanyoyi da masana'antu domin jihar ta zama abar kwatance a kasar nan dama duniya baki daya.

A karshe ya nemi goyon bayan al'ummar jihar akan su hada karfi da karfe wurin kawo cigaba ga jihar, sannan kuma hakanne zai bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje damar gabatar da ayyukan da ya saka a ranshi na alkhairi ta hanyar yin shawarwari da mutanen jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel