Gwamnan Adamawa bai yarda da zaben 2019 ba, ya tafi gaban Kotu

Gwamnan Adamawa bai yarda da zaben 2019 ba, ya tafi gaban Kotu

Gwamnan jihar Adamawa wanda ke kan karagar mulki har zuwa karshen watan gobe, Jibrilla Bindow, ya sheka gaban kotun da ke sauraron karar zabe, bayan ya sha kayi a hannun jam’iyyar PDP.

Mohammad Jibrilla Bindow ya samu ya kai kara gaban kotun da ke sauraron korafin zabe a Najeriya, inda yake neman a soke zaben gwamna da aka yi a jiharsa wanda Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP ya lashe zaben.

Mai girma Bindow ya fadawa kotu a bayyana cewa shi ne ya ci zaben 2019 ko kuma a sake gudanar da wani sabon zabe. Bindow ya kafa hujja ne da cewa an tafka magudi iri-iri a kananan hukumomi 7 a lokacin zaben jihar.

KU KARANTA: Lauyoyin PDP sun fusata bayan INEC ta gagara mikawa Atiku kayan zabe

Gwamnan Adamawa bai yarda da zaben 2019 ba, ya tafi gaban Kotu

Gwamna Bindow da ya sha kasa a zaben 2019 yayi amai ya lashe
Source: Depositphotos

Hukumar zabe ta tabbatar da cewa PDP ce ta lashe zaben jihar Adamawa inda Ahmadu Umaru Fintiri ya samu kuri’a 376,552, yayin da shi kuma gwamna Jibrilla Bindow mai-ci wanda yayi takara a APC mai mulki ya samu kuri’u 336,386.

Tuni dai har gwamnan ya taya Abokin hamayyarsa Umaru Fintiri murnar lashe zaben na bana, sai kuma aka ji kwatsam, ya shigar da kara gaban Alkali inda yake nema a rushe zaben da aka yi a sake gudanar da wani danyen zabe a Jihar.

KU KARANTA: 2019: Ma’aikatan INEC za su taimakawa Atiku a Kotun karar zabe

Shugaban jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Gabas, Umar Duhu, ya bayyana cewa sun gano cewa ba a bi gaskiya wajen zaben na bana ba. Duhu yace binciken da su kayi, ya nuna masu cewa an yi abubuwan da su ka sabawa dokar zabe.

Umar Duhu wanda babban na-kusa da gwamna Jibrilla Bindow ne ya bayyana cewa za su tafi kotu da kwararan hujjoji. Duhu yake cewa su na da yakinin cewa kotu za ta karbe zaben ta ba jam’iyyar APC nasara muddin ta ga tarin hujjojin su.

Jigon na APC yayi wannan jawabi ne a Ranar Talata 23 ga Watan Afrilu a cikin babban birnin Adamawa na Yola. Duhu ya kuma zargi wasu daga cikin Iyalan shugaban kasa Buhari da taimakawa jam’iyyar adawa ta PDP wajen lashe zaben jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel