A karshe dai hukumar NYSC ta yi magana akan karin kudin 'yan bautar kasa

A karshe dai hukumar NYSC ta yi magana akan karin kudin 'yan bautar kasa

- Hukumar NYSC ta fito ta karyata jita-jitar da ake yadawa a kafar sadarwa ta zamani da ke nuni da cewa gwamnati ta kara 'yan bautar kasar albashi daga N19,800 zuwa N31,800

- Hukumar ta ce wannan zance ba shi da tushe bare makama, kuma in dai har akwai maganar karin kudin ita ya kamata ta sanar da jama'a ba wasu ba

Hukumar 'yan bautar kasa (NYSC) ta karyata jita-jitar da ake yadawa a kafofin yada labarai da ke nuna cewa za a karawa 'yan bautar kasan kudi daga N19,800 zuwa 31,800, bayan shugaban kasa ya sanya hannu a dokar karawa ma'aikata kudi a kasar nan.

Mataimakin Darakta na hukumar na kasa Eddy Megwa, ya shaidawa manema labarai a jiya Laraba cewa gwamnatin tarayya ba ta sanar da shirin karawa 'yan bautar kasar kudi ba.

A karshe dai hukumar NYSC ta yi magana akan karin kudin 'yan bautar kasa

A karshe dai hukumar NYSC ta yi magana akan karin kudin 'yan bautar kasa
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa, ko da yake ba hukumar NYSC ba ce ta ke biyan 'yan bautar kasar kudin su ba, amma ya san da cewa gwamnatin tarayya za ta sanar da su idan ma akwai shirin karawa 'yan bautar kasar kudi wanda ya wuce N19,800 da aka saba biyansu, ya ce da gwamnati ta sanar da karin za su sanar da kowa halin da ake ciki.

KU KARANTA: Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi

Ya ce, "Ba hukumar NYSC ba ce ta ke biyan 'yan bautar kasa kudin su ba, gwamnatin tarayya ce. Har sai gwamnati ta gama shirin ta na karawa ma'aikata albashi zuwa N30,000, saboda haka ba za mu iya fadin abinda gwamnati za ta dinga biyan 'yan bautar kasa ba.

"Ku yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa a kafafen sadarwa. Idan gwamnatin tarayya ta shirya kara muku albashi za ta yi mana magana, mu kuma za mu sanar da ku duk halin da ake ciki."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel