An kama mutanen da suka kashe 'yan sanda hudu da mata mai ciki

An kama mutanen da suka kashe 'yan sanda hudu da mata mai ciki

- Hukumar 'yan sanda ta samu nasarar kama 'yan ta'addar nan da suka kashe jami'an 'yan sanda hudu da wata mata mai ciki, kuma suka sanyawa ofishin hukumar 'yan sandan wuta

- An kama 'yan ta'addar ne sanadiyyar karbar wayar daya daga cikinsu da aka yi, inda aka gano cewa ta daya daga cikin 'yan sandan da aka kashe ne

A jiya Laraba ne 24 ga watan Afrilu aka kama mutanen nan da suka kashe 'yan sanda hudu da wata mata mai ciki a ofishin 'yan sanda na Afuze dake karamar hukumar Owan cikin jihar Edo, a ranar 12 ga watan Maris din da ta gabata.

Wadanda ake zargin sun hada da, Agunu Ernest mai shekaru 24, Paul Richard mai shekaru 24, Sunday Thank God mai shekaru 21, Suleiman Omogbai mai shekaru 22, George Sebastian mai shekaru 20, da kuma Agbomikhe Agustine mai shekaru 22, sun kashe jami'an 'yan sandan guda hudu, suka sanyawa ofishin 'yan sandan wuta, sannan suka saki 'yan uwansu, wadanda aka kama da laifin fashi da makami a yankin.

An kama mutanen da suka kashe 'yan sanda hudu da mata mai ciki

An kama mutanen da suka kashe 'yan sanda hudu da mata mai ciki
Source: UGC

Mutanen sun zo hannu ne bayan wani jami'in dan sanda ya karbi wayar daya daga cikin su mai suna Agunu Ernest sai ya ga cewa mafi yawan lambobin kan wayar na 'yan sanda ne. A karshe dai Ernest ya bayyana cewa wayar ta daya daga cikin 'yan sandan da suka kashe ne a ofishin 'yan sanda na Afuze.

KU KARANTA: Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi

A wata hira da ya yi da manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargin, Suleiman Omogbai, ya ce Ernest wanda jami'an 'yan sanda suka kama shine ya gayyace su akan su zo su kwato su daga hannun 'yan sandan. Ya ce Abaga ne ya kawo bam din da suka yi amfani da shi a ofishin 'yan sandan, ya kara da cewa ba su da niyyar kashe 'yan sandan, amma bai san yadda aka yi suka kashe 'yan sandan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel