Majalisar dattijai ta ki amincewa da Kogi a matsayin jihar dake da man fetur

Majalisar dattijai ta ki amincewa da Kogi a matsayin jihar dake da man fetur

-Tarihi ya nuna cewa jihar Kogi tana da danyen man fetur

-Kujerar naki! majalisar dattijai ta ki amincewa da kudirin bayyana jihar Kogi a matsayin jiha dake da arzikin dayen man fetur

Majalisar dattijai ta ki amincewa da kudrin cewa jihar Kogi na daya daga cikin jihohi dake da man fetur a kasar nan. Yayinda da majalisar ke zamanta da ta saba ranar Laraba, sanata Isaac Alfa mai wakiltar Kogi ta gabas ya kawo wannan kudurin.

Akwai bukatar cewa an tabbatar da Kogi a matsayin jiha wacce take da man fetur. Kamfanonin man fetur irinsu Shell da Total sun fara hako man ne tun shekarar 1952 a wasu kauyukan dake karamar hukamar Ibaji ta jihar Kogi.

Majalisar dattijai ta ki amincewa da Kogi a matsayin jihar dake da man fetur

Majalisar dattijai
Source: UGC

KU KARANTA:Akan cin hanci da rashawa Buhari yayi dan kokari kadan, inji Wole Soyinka

Yace zai iya tunawa kamfanonin sunyi nasarar hako rijiyoyi kanana 25 da kuma asalin manyan rijiyoyin guda 8 da ke Anambra. Duk da hakan, mafi yawancin rijiyoyin suna jihar Kogi.

Ya kara da cewa: “Wadannan bayanai an rubutasu a cikin wata wasika da aka aikawa shugaban kasa ta hannun tsohon manajan NNPC, Sam A. Uchola ranar 21 ga watan Nuwamban 2003.”

Alfa yace duk wani aikin hakar mai a jihar Kogi ya tsaya cak sai zuwa 18 ga watan Yulin 2001 yayinda tsohon gwamanan jihar, Abubakar Audu ya rubata wasika zuwa jagoran NNPC domin ya tuna cewa an fa samu danyen man fetur a Odeke, Echeno da kuma Anocha.

Majalisar ta hau kujerar naki bisa wannan kudurin da aka kawo mata, inda da dama cikin wadanda sukayi magana akan wannan batu, cewa sukayi an dau tsawon lokaci ba tare da an hako danyen man fetur ba a jihar Kogi. Akwai bukatar jihohin Anambra, Kogi da Enugu su sasanta tsakaninsu kan abinda ya shafi kan iyakar jihohin nasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel