Majalisa ta 9: Bana tunanin APC ta koyi darasi daga kuskurenta na 2015 - Sani

Majalisa ta 9: Bana tunanin APC ta koyi darasi daga kuskurenta na 2015 - Sani

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Mista Shehu Sani, yace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bata koyi darasi daga abunda ya faru a 2015 ba wanda yasa Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara suka zamo Shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai.

Yayinda ya bayyana a shirin Channels TV na Politics Today, Sani ya bayyana cewa ra’ayin sauran yan majalisa na APC a wajen shugabancin majalisar dokoki na tara na iya haifar da maimaicin abunda ya faru shekaru hudu da suka gabata.

Furucin Sanin a zuwa ne wata daya bayan Shugaban APC, Adams Oshiomole, yace jam’iyyar ba zata bari yan majalisa daga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) su jagoranci kowani kwamiti na majalisa mai zuwa ba.

Majalisa ta 9: Bana tunanin APC ta koyi darasi daga kuskurenta na 2015 - Sani

Majalisa ta 9: Bana tunanin APC ta koyi darasi daga kuskurenta na 2015 - Sani
Source: Twitter

Oshiomhole yayi bayanin cewa hukuncin jam’iyyar don guje ma abunda ya faru a 2015 ne, inda ya kara da cewa sun koyi darasi daga kura-kuransu.

Da yake martani ga furucin Oshiomhole, Sani ya bayyana cewa kafin a zabi mutum a matsayin Shugaban majalisar dattawa “gasa ne dake bukatar adadin mutane.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Ingila a yau

Sani wanda ya sauya sheka zuwa People’s Redemption Party (PRP) yan kwanaki kafin zaben 2019 daga jam’iyya mai mulki, ya bayyana cewa idan har ana son dan takarar da APC ta fi so yayi nasara, ya zama dole a nemi yan majalisa na jam’iyyar adawa sannan a shiga yarjejeniya dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel