Gwamnatin Buhari ta bayyana babban matsalar da take fuskanta a yaki da ta’addanci

Gwamnatin Buhari ta bayyana babban matsalar da take fuskanta a yaki da ta’addanci

Gwamnatin Najeriya ta bayyana babban kalubalen da take fuskanta a yakin da take yi da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, inda ta danganta wannan kalubale ga karancin jami’I a hukumomin tsaron Najeriya.

Babban mashawarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan harkar watsa labaru, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace karancin jami’an tsaro yasa ba a kowane gari ko kauye ake samun jami’an tsaron ba.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da jami’an hukumar bada agajin gaggawa 4

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Garba yana cewa “Matsalar itace ba’a samun jami’an tsaro na tsawon sa’o’i 24 a kauyuka ko garuruwa, wannan kuma ya samo asali ne daga karancin adadinsu.”

Sai dai Garba ya yaba tare da jinjina ma dakarun rundunar Sojojin hadaka ta kasa da kasa dake aikin yaki da Boko Haram a jahar Borno, inda yace suna matukar kokari, kuma aikinsu na kyau.

Haka zalika Malam Garba ya koka kan karancin isassun kudade a yakin da Sojoji suke yi da Boko Haram, amma ya daura wannan laifi kacokan akan majalisar dokokin Najeriya, inda yace tayi biris da bukatar shugaban kasa na diban dala biliyan daya daga asusun raran man fetir don sayan ma Sojoji makamai.

Daga karshe kaakakin shugaba Buhari ya tabbatar da nasarar da Sojoji suke samu a yakin da suke yi da yan bindigan jahar Zamfara, sai dai ya nemi shuwagabannin addinai da kuma shuwagabannin al’umma dasu basu gudunmuwa ta hanyar bayyana musu bayanai sahihai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel