Addu’a na Buhari ya zakulo kwararru wannan karo – Inji Fasto Bakare

Addu’a na Buhari ya zakulo kwararru wannan karo – Inji Fasto Bakare

Babban Faston nan na cocin Latter Rain Assembly, Tunde Bakare, ya bayyana cewa yana addu’a shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wadanda su ka cancanta a gwamnatinsa wannan karo.

Tunde Bakare wanda yayi takara a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da shugaba Buhari a karkashin jam’iyyar CPC a 2011, yana so ya ga Buhari ya dauko wadanda su ka san aiki, ya ba su mukami a wa’adin nan na sa na biyu.

‘Dan takarar na mataimakin shugaban kasa a zaben 2011 yana so Buhari ya nemi wadanda su ka san aiki a gwamnatin sa ne domin ganin kasar ta cigaba. Bakare yana ganin cewa Najeriya tana da isassun kwararrun da za su iya yin aiki.

Faston yake cewa akwai matukar bukatar a samawa dinbin Matasan kasar aiki domin ganin an rage aikata laifuffuka a fadin kasar. Bakare yake fadawa Channels TV cewa akwai matsala idan ya zama miliyoyin matasa ba su da abin yi.

KU KARANTA: Rikicin Boko Haram ne babbar matsalar Gwamnatin Buhari

Addu’a na Buhari ya zakulo kwararru wannan karo – Inji Fasto Bakare

Bakare ya ba Shugaban kasa Buhari shawara yayi aiki da kwararru
Source: Depositphotos

Bakare ya nanata bukatar samawa Matasa aikin yi, sannan kuma ya koka da halin da harkar ilmi yake ciki a yau. Malamin addinin kuma babban ‘dan siyasar yake cewa ana bukatar gwamnatin Najeriya ta dawo da martabar ilmi a kasar.

A jawabin na sa, Bakare ya soki yawan bude sababbin jami’o’i da ake yi a kasar inda yace wadannan makarantu ba su da banbanci da sakandare, don haka yake kira gwamnati ta fi maida karfi wajen gyara makarantun da ake da su.

Haka zalika Tunde Bakare yace tarin Almajiran da ake da su a Najeriya wadanda ba su da wani ilmin kirki, kuma su ke fama da talauci, za su zama matsala a Najeriya nan gaba don haka ya nemi a shawo kan matsalar bara a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel