Gwamnatin Saudiyya zata gina matatar mai ta zamani a Najeriya

Gwamnatin Saudiyya zata gina matatar mai ta zamani a Najeriya

Gwamnatin kasar Saudi Arabia ta bayyana burinta na gina katafaren matatar man fetir a Najeriya, kamar yadda ministan harkar man fetir na kasar, Khalid Al-Falih ya bayyana a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Minista Al-Falih ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da karamin ministan harkar man fetir na Najeriya, Ibe Kachikwu a babban birnin kasar Saudiya, Riyadh inda ya gana da shuwagabannin hukumar man fetirin Najeriya.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da jami’an hukumar bada agajin gaggawa 4

Gwamnatin Saudiyya zata gina matatar mai ta zamani a Najeriya

Kachikwu
Source: Depositphotos

Shima a jawabinsa, Mista Ibe ya bayyana farin cikinsa da wannan bukata ta kasar Saudiyya, inda yace akwai bukatar kasar ta cika wannan buri nata na gina matatar man fetir a Najeriya, musamman duba da dimbin amfanin da Najeriya zata samu daga wannan muhimmin aiki.

“Muna fatan cin gajiyar babbar nasarar da gwamnatin kasar Saudiyya ta samu a harkar man fetir, inda a shekarar data gabata kadai kamfanin man Saudiyya, Aramco ya samu ribar dala biliyan dari biyu ($200,000,000,000)!

“Muna da alaka da yawa da Saudiyya, ta bangaren tarihi, ta bangaren addini, don haka akwai bukatar mu karfafa alakarmu a kungiyar kasashe masu arzikin man fetir na OPEC, musamman a harkar daya shafi man fetir.” Inji shi.

Ministan ya kara da cewa tuni Najeriya ta kafa kwamiti da zata tattauna da kasar Saudiyya tare da ganin an wajen cimma wannan manufa da tasa a gaba na habakka dangantakar dake tsakanin Najeriya da Saudiyya ta bangaren abinda ya shafi zuba hannun jari a sha’anin man fetir.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan muhimmin taro akwai shugaban kamfanin man fetirin Saudiyya, watau Aramco, Amin H Nasser, da sauran shuwagabannin kamfanin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel