A nada sakataren gwamanatin tarayya daga bangaren Igbo, wani dan majalisar wakilai ya roki Buhari

A nada sakataren gwamanatin tarayya daga bangaren Igbo, wani dan majalisar wakilai ya roki Buhari

-Yankin Igbo na ganin an barsu baya a wannan gwamnati

-Zaiyi matukar wahala ya kasance sakataren ya fito daga bangaren Igbo, masu iyawa magana na cewa "yaba kyauta tukwici" basu zabi APC ba

Hon. Tony Nwoye (APC, Anambra) ya roki shugaba Buhari cewa yayinda zai nada sabon sakataren gwamnatin tarayya da ya dauko shi daga yankin na kudu maso gabas, yankin da shi wannan dan majalisa ya fito kenan.

Nwoye, wanda ke wakiltar Anambra ta gabas da kuma yamma yayi wannan kiran ne yayinda da ya halarci wani taro na karfafa matasa a garin Nsuge wanda ke kusa da Onicha ranar Laraba.

Har wa yau, dan majalisar wanda tsohon dan takarar gwamna ne a jihar Anambra karkashin jam’iyar APC yace yin hakan zai dawo da martabar APC a yankin nasu.

A nada sakataren gwamanatin tarayya daga bangaren Igbo, wani dan majalisar wakilai ya roki Buhari

Hon. Tony Nwoye
Source: UGC

KU KARANTA:Shugaban kasa Buhari ya je Legas bai hadu da Bola Tinubu ba

“ Mutanenmu na jin cewa an waresu. Ba a dauki Igbo da kima ba cikin harkokin kasar nan. Bai kamata ace an waremu saboda kawai bamu zabi Buhari ba, abinda ya kasance son kai da kuma ra’ayine na yan yankin.

“ Yankin kudu maso gabas ya cancanci sakataren tarayya ko kuma mataimakin shugaban majalisar dattijai. A matsayin shugaban Buhari na mutum mai hangen nesa da sanin ya kamata wanda kuma har ila yau yake dauka yan Najeriya matsayin abu guda, yakamata ya sanya Igbo su kasance cikin wannan tafiya tashi.”

Ya kara da cewa yin hakan zai karfafa APC a yankin ta yanda zata iya lashe zabe a yankin nan gaba. Bugu da kari, ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa ga aikin titin da tayi a gundumar da yake wakilta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel