Shugaban kasa Buhari ya je Legas bai hadu da Bola Tinubu ba

Shugaban kasa Buhari ya je Legas bai hadu da Bola Tinubu ba

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a jiya Laraba 24 ga Watan Afrilu inda ta ce tun da jirgin da ya kawo shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya iso Legas, har ya koma, bai hadu da Asiwaju Bola Tinubu ba.

Shugaba Muhammadu Buhari yana Legas jiya tun da kimanin karfe 10:30 na safe har zuwa kusan 3:20 na yamma, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar a karkashin jagorancin gwamna Akinwunmi Ambode tayi.

Kamar yadda labarai su ka zo mana, babu wanda ya ga babban jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu wajen wannan ziyara da shugaban kasa ya kawo. Gwamnonin Kudu na yamma ne dai su ka tarbo shugaban kasar jiya.

KU KARANTA: Buhari ya jinjinawa kokarn Gwamnan Jihar Legas

Gwamnan Legas Akinwumi Ambode, Abiola Ajimobi, da kuma Rotimi Akeredolu, ne su ka karbi shugaban kasar da tawagarsa a babban filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke cikin Garin na Legas inda ya zo ya yini a jihar.

Gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da Takwaransa Ibikunle Amosun na Ogun ne su ka raka shugaban kasar ya hau jirgi ya koma fadarsa da yammacin jiya. Sai dai har a wannan lokaci ba a hangi Bola Tinubu a kusa da jirgin shugaban kasar ba

KU KARANTA: Mace ta fito takarar kujerar Majalisar Wakilai a APC

Daga cikin wadanda su ka takawa shugaban kasa Buhari baya a lokacin da zai koma akwai gwamna mai jiran-gado a Legas, Babajide Sanwo-Olu, da kuma mataimakinsa Obafemi Hamzat da sauran wasu manyan jiga-jigan siyasar jihar Legas.

Rashin Tinubu wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne a wajen wannan taro ya ba jama’a mamaki. Tinubu bai bada wani dalili na rashin zuwansa ba. Sai dai kwanaki shi ma shugaba Buhari bai halarci bikin taya ‘dan siyasar cika shekara 67 ba.

Bola Tinubu ya sa rai cewa shugaba Buhari zai halarci bikin da aka shirya a Ranar da ya cika shekaru 67 a Duniya kamar yadda ya saba. A lokacin har Tinubu ya tsara jawabinsa da sunan shugaba Buhari a ciki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel