Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da jami’an hukumar bada agajin gaggawa 4

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da jami’an hukumar bada agajin gaggawa 4

Wasu gungun yan bindiga sun bude wuta akan jami’an hukumar bada agajin gaggawa watau NEMA, inda suka yi awon gaba da mutane hudu daga cikinsu da nufin karbar kudin fansa daga wajen iyalansu kafin su sake.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu a karamar hukumar Abua-Odual, kamar yadda shugaban hukumar a yankin kudu masu kudu, Walson Branden ya tabbatar a garin Fatakwal.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000

Mista Walson ya bayyana cewa yan bindigan sun kai ma ma’aikatan farmaki ne a yayin da suke kididdigan manoman da ambaliyan ruwa ya shafa a jahar da nufin basu tallafin daya dace don su cigaba da sana’arsu.

A daidai wannan lokaci ne yan bindigan suka bayyana, inda suke bude musu wuta har suka samu guda daga cikin ma’aikatan da harsashi a kafarsa, amma duk da haka sai da ya samu ya tsallake rijiya da baya, yayin da suka yi awon gaba da sauran ma’aikata guda hudu, daga cikinsu har da wata Mace.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa rashin kyawun motar da ma’aikatan ke ciki ne yasa yan bindigan suka samu nasarar yin garkuwa dasu cikin sauki ba tare da sun sha wani wahala ba.

Sai dai da aka tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Omoni Nnamdi don jin ta bakinsa game da lamarin, sai yace bai samu wani rahoto makamancin wannan har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel