Shugabancin majalisa: Gbajabiamila ya samu goyon bayan Sheikh Dahiru Bauchi (Hotuna)

Shugabancin majalisa: Gbajabiamila ya samu goyon bayan Sheikh Dahiru Bauchi (Hotuna)

Shahararren Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana goyon bayansa ga dan majalisa Femi Gbajabiamila a kokarinsa na darewa kujerar Kaakakin majalisar wakilai a sabuwar majalisa ta Tara.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Shehin Malamin ya bayyana goyon bayan nasa ga Femi Gbajabiamila ne a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu yayin da suka hadu a farfajiyar Masallacin Makkah dake kasar Saudiyya inda suka tafi zuwa aikin Umarah.

Shugabancin majalisa: Gbajabiamila ya samu goyon bayan Sheikh Dahiru Bauchi (Hotuna)

Shugabancin majalisa: Gbajabiamila ya samu goyon bayan Sheikh Dahiru Bauchi
Source: Facebook

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kebbi zata gudanar da aikin ido kyauta ga mutane 1000

Shi dai Femi, shine wakilin al’ummar mazabar Surulere a majalisar wakilai, kuma wannan ne karo na biyar da yake majalisar wakilan, don haka yake ganin karansa ya kai tsaiko na ya zama kaakakin majalisar, musamman duba da cewa ya fito ne daga jam’iyyar APC.

Shugabancin majalisa: Gbajabiamila ya samu goyon bayan Sheikh Dahiru Bauchi (Hotuna)

Gbajabiamila
Source: Facebook

Wannan goyon baya da Gbajabiamila ya samu daga wajen Shehin Malami Dahiru Usman Bauchi ya kasance guda daga ire iren goyon bayan da yake samu daga jama’a daban daban don ya gaji Yakubu Dogara.

Ana sa ran dan majalisar zai dawo Najeriya cikin yan kwanakin nan domin ya cigaba da gwagwarmayar darewa mukamin kaakakin majalisar kafin ranar rantsar da sabbin yan majalisa ta 9 a ranar 10 ga watan Yuni.

Daga cikin wadanda suka raka dan majalisan zuwa Umarah akwai Manur Manu Soro, dan majalisa dake wakiltar al’ummar mazabar Darazo da Ganjuwa a majalisar wakilai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel