Atiku ya lalubo Ma’aikatan zabe cikin masu masa shaida a Kotu

Atiku ya lalubo Ma’aikatan zabe cikin masu masa shaida a Kotu

Akalla mutane 12 da su kayi wa hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta, INEC, aiki a zaben 2019 da ya gabata ne za su tsayawa ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar, a kotun da ke sauraron karar zabe.

Premium Times ta rahoto cewa wadansu Ma’aikatan INEC da aka yi amfani da su a zaben 2019, za su je gaban kotu su rantse cewa sun yi aiki da na’uran zamani wajen aika sakamakonnin zaben shugaban kasa a zaben da ya gabata.

Atiku Abubakar yana korafin cewa shi ya lashe zaben 2019 kamar yadda alkaluman da ke cikin na’urorin ajiyan kuri’un da INEC ta ke amfani da su, su ka nuna. Atiku yace a zahiri shi ya lashe zaben na bana da kuri’u 18,356,732.

Ita kuwa INEC ta karyata cewa tayi aiki da na’urori wajen tattara kuri’u a zaben 2019. Wannan ya sa Atiku Abubakar ya nemo wadanda su kayi aiki da INEC a zaben da su ka shirya zuwa kotu su rantse da cewa an yi amfani da na’urorin.

KU KARANTA: Hukumar INEC ta gagara mikawa Atiku kayan aikin zabe

Atiku ya lalubo Ma’aikatan zabe cikin masu masa shaida a Kotu

Wadanda su kayi wa INEC aiki za su zama shaidun Atiku Abubakar a Kotu
Source: Facebook

‘Dan takarar na PDP yace wani ‘dan cikin-gidan INEC ne ya fito masa da sakamakon zaben daga cikin na’urorin adanar INEC. Atiku Abubakar ya kuma bayyana lambobin wadannan na’urori domin ya karawa hujjar sa karfi a gaban kotun zabe.

Bayan INEC ta karyata cewa ta tura sakamakon zabe ta na’urorin zamani ne Lauyoyin Atiku su ka bankado karin hujjojinsu, inda aka ga cewa su na takardun shaidar ma’aikatan 12 da su ka nuna akasin abin da hukumar INEC ta ke ikirari.

Ita dai INEC ta sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zabe da kuri’u 15,191,847, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar hamayya ta PDP ya tashi da kuri’a 11,262,978 a zaben na 2019.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel