Duk da umarnin Kotu, INEC ta ki ba mu kayan zabe domin mu duba – Atiku Abubakar

Duk da umarnin Kotu, INEC ta ki ba mu kayan zabe domin mu duba – Atiku Abubakar

Lauyoyin da ke kokarin karbowa Atiku Abubakar da Peter Obi nasara a kotun sauraron karar zabe na 2019, su na kuka da yadda hukumar zabe na INEC ta ki ba ta kayan aikin zabe domin ta duba.

Duk da kotun daukaka kara a Najeriya ta bada umarni ga INEC ta ba Lauyoyin ‘dan takarar PDP, Atiku Abubakar, kayan da aka yi amfani da su wajen gabatar da zaben 2019 ta tayi bincike, har yanzu INEC ba ta cika wannan umarni ba.

Silas Onu wanda yana cikin manyan Lauyoyin da ke kare Atiku Abubakar da Peter Obi ya fadawa gidan jaridar Channels TV cewa an hana su ganin wadannan kaya na zabe duk da cewa sun cika sharuda har sun kuma biya kudin aiki.

KU KARANTA: Manayn Kungiyar Izala sun bar Najeriya bayan zaben 2019

Duk da umarnin Kotu, INEC ta ki ba mu kayan zabe domin mu duba – Atiku Abubakar

Lauyoyin Atiku su na kokawa da taurin kan hukumar INEC
Source: UGC

Lauyan yake cewa ganawa da masu kare hukumar INEC a gaban kotun yana nema ya zama masu wahala, amma ya sha alwashin cewa za su cigaba da kokarin ganin hukumar ta cika umarnin da aka ba ta na ba su kayan zaben na 2019.

Sai dai Silas Onu yana ganin cewa idan wannan lamari ya ci tura, za su nemi su maka shugaban hukumar zaben mai zaman kan-ta da kuma sauran manyan jami’an hukumar a gaban kuliya da laifin bijirewa umarnin babban kotu.

Wani babban jami’in INEC a Najeriya, Oluwole Osaze-Uzzi, ya musanya wannan koke-koke da PDP ta ke yi, inda ya nemi jam’iyyar adawar ta sake komawa gaban kotu da shigar da wani danyen kara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel