Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Birtaniya a yau

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Birtaniya a yau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu bayan ya ziyarci Maiduguri, jihar Borno, ofishin labaransa ta bayyana.

A ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu ne Shugaban kasar ya ziyarci Lagas inda ya kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta aiwatar.

"A yanzu zai je Maiduguri domin kaddamar da ayyuka na musamman a fannin ilimi, lafiya da kuma hanyoyi,” a cewar Femi Adesina, kakakin Shugaban kasar.

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Ingila a yau

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari zai tafi kasar Ingila a yau
Source: UGC

"Daga nan Buhari zai garzaya kasar Ingila kuma zai kasance a chan har zuwa ranar 5 ga watan Mayu bisa ziyarar kai,” Femi Adesina ya kara sanarwa.

Sanarwar ya zo kamar haka: “A ci gaba da ziyarar aiki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Lagas a ranar Laraba inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar, Shugaban kasar na shirin zuwa Maiduguri, babbar birnin jihar Borno domin ziyarar wani aiki a ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta bayyana babban matsalar da take fuskanta a yaki da ta’addanci

“Ana sanya ran zai kaddamar da wasu ayyukan ci gaba musamman a fannin ilimi, lafiya da hanyoyi.

“A karshen ziyarar, Shugaban kasar zai garzaya kasar Birtaniya a kan ziyarar kai. Ana sanya ran zai dawo Najeriya a ranar 5 ga watan Mayu, 2019.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel