Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutum 2 a kauyen Kaduna

Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutum 2 a kauyen Kaduna

- Yan bindiga sun hallaka mutum 2 a garin Ambe Madaki da ke jihar Kaduna

- Shugaban karamar hukumar, Mista Charles Danladi ya tabbatar da afkuwar Lamarin

- Ya yi korafin cewa kashe-kashe ya zama rowan dare a yankin

Wasu yan bindiga a daren ranar Lahadi sun kashe akalla mutum biyu a Ambe Madaki da ke masarautar Gwantu a karamar hukumar Sanga na jihar Kaduna.

Daga cikin wadanda abun ya cika dasu akwai Ibrahim Manzo dan shekara 70 da kuma dan dan’uwansa Barnabas Musa mai shekara 45.

Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutum 2 a kauyen Kaduna

Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun kashe mutum 2 a kauyen Kaduna
Source: UGC

Shugaban karamar hukumar, Mista Charles Danladi ya tabbatar da afkuwar Lamarin a jiya, Laraba, 24 ga watan Afrilu inda ya bayyana abun a matsayin abun bakin ciki.

Yayinda yake ta’aziya da jaje ga iyalan wadanda abun ya shafa, Shugaban karamar hukumar yayi korafin cewa kashe-kashe ya zama rowan dare a yankin.

KU KARANTA KUMA: Buratai ya kaddamar da sabon katafaren ginin makaranta a hedikwatar soji a Jaji (Hotuna)

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa mutane goma sha tara ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya faru a karamar hukumar Gwaram cikin jihar Jigawa a jiya 23 ga watan Afrilun shekarar 2019.

An ce mutanen cikin motar sun kone kurmus, ta yadda ba a iya gane su, inda kadan daga cikin su, da jariri guda daya suka ji rauni.

Mun samu rahoton cewa jaririn ya kubuta ne, bayan da mahaifiyarsa ta jefo shi daga cikin motar a dai dai lokacin da lokacin da motar ta ke shirin faduwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel