Na gamsu da ayyukan Ambode, inji Buhari

Na gamsu da ayyukan Ambode, inji Buhari

-Ambode yayi matukar birge shugaba Buhari

-Yayin ziyarar muhimman ayyukan har guda uku da Ambode yayi a Legas sune shugaba Buhari ya kaddamar inda ya baro Legas cike da farin ciki

Shugaba Buhari yayin da kai ziyara birnin Legas ya kaddamar da ayyuka muhimmai guda uku.

Buhari ya ji dadi kwarai da gaske ganin wadannan ayyukan da Ambode yayiwa jihar tasa na cigaba cikin kankanin lokaci. Sam bai boye farin cikinsa ba kan wannan al'amari inda ya yabawa gwamnan kan namijin kokarin da yayi.

Daga cikin ayyukan akwai, tashar mota bas ta zamani a Oshodi, sai kuma tashar bas domin zirga-zirga daga Legas zuwa wasu jihohi da kuma filin jirgin saman Murtala Mohammed da gwamnan ya gyara hanyar zuwa filin.

Na gamsu da ayyukan Ambode, inji Buhari

Buhari a jihar Legas
Source: UGC

KU KARANTA:Jami’o'i 7 sun samu sabbin cibiyoyin bincike mai zurfi

A cewar shugaba Buhari: “Kamar yanda wannan tashar ta zamani zata bunkasa sha’anin zirga-zirgar mutane a cikin garin Legas. Hakan cigaba ne mai matukar muhimmanci wanda zai kawo saukin zirga-zirga a cikin jihar inda gwamnatin ta samar da bas 820 domin aikin.

“ Hakika wadannan ayyuka da gwamnatin Legas keyi sun zo daidai da na gwamnatin tarayya bisa kudurinta na kawo cigaba a Najeriya musamman fannin safara. Domin karfafa tashar ta Oshodi gwamnatin tarayya ta bada aikin babbar hanyar Apapa-Oshodi har zuwa Oworonshoki wacce ta kai shekara 40 rabon da a waiwayeta.

“ Aikin titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan na nan yana cigaba da gudana. Baza muyi kasa a gwiwa ba saboda farin cikin al’umma shi mu kasa a gaba. A don haka ayyuka irin wadannan yanzu muka fara.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel