Ministar kudi ta fadi dalilin da yasa gwamnati ba ta iya kaddamar da kasafin kudi a shekara

Ministar kudi ta fadi dalilin da yasa gwamnati ba ta iya kaddamar da kasafin kudi a shekara

Gwamnatin tarayya ta koka a kan yadda gibi a bangaren kudaden shigowa ke hana ta kaddamar da kasafin shekara kamar yadda ya ke a cikin bajet.

Mai taimakawa ministar kudi a bangaren sadarwa da yada labarai, Mista Paul Ella Abechi, ya bayyana cewar samun gibi a kudaden da ke shiga aljihun gwamnati na matukar damun ministar.

A cewar Abechi, ministar tayi amanna cewar rauni wajen kudaden dake shiga aljihun gwamnati ne babban kalubale ga kaddamar da kasafin shekara kamar yadda gwamnati ke tsara wa kowacce shekara.

"Matsalar kudaden shiga ne ke saka gwamnati ta gaza cimma dukkan tanade-tanaden da tayi a cikin kasafinta na shekara. Hakan ne yasa ba ma iya kammala manyan aiyuka, biyan albashi da alawus da kuma biyan bashin da ake bin gwamnati," a cewar Ministar.

Ministar kudi ta fadi dalilin da yasa gwamnati ba ta iya kaddamar da kasafin kudi a shekara
Ministar kudi; Zainab Ahmad
Source: UGC

Ministar na wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi a kan kudaden shiga da kasa ke samu (IGR) da kuma bashin da ake bin Najeriya, a wurin wani taro a kan harkar tattalin arziki da bankin duniya da hadin gwuiwar IMF suka dauki nauyin gudanar da shi a kasar Amurka.

DUBA WANNAN: Cin kudin Atiku: PDP ta dakatar da shugaba da mataimakin jam'iyyar a jihar Filato

Ministar ta kara da cewa: "abinda muke yi ma'aikatar kudi shine mayar da hankali wajen inganta harkokin shigowar kudi aljihun gwamnati."

Kazalika, ministar ta nuna farincikinta a kan yadda har yanzu bashin da ake bin Najeriya ya tsaya a kaso 19% idan aka kwatanta da habakar tattalin arziki a cikin kasa (GDP).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel